Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayar da umarnin a yi dukkan kokarin da ya kamata na bincike da ceton mutanen da suka bace sanadiyyar zaftarewar laka da ta auku a Nepal, wadda ta shafi mutane a Gyirong da ke kan iyakar Nepal da Sin, a jihar Xizang mai cin gashin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli mai kula da harkokin soja, ya bukaci a yi kokarin kwashe mazaunan da ke cikin hadari da bayar da kulawar lafiya a kan lokaci ga wadanda suka jikkata domin rage radadin ibtila’in. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
ADVERTISEMENT