Gargadi: Wannan labarin na kunshe da bayanan da za su iya tayar da hankalin mai karatu Mohammed Amin ya rasu yana da shekara takwas, jim kadan bayan gwaji ya nuna cewa yana dauke da cutar HIV mai karya garkuwar jiki.
Ya rika yin zazzabi mai zafi da muni inda a wani lokaci ya kan so ya kwanta a cikin ruwan sama, yana cikin ”tsananin ukuba tamkar wanda aka jefa a kaskon suya,” in ji mahaifiyarsa, Sughra.
Kwanaki kadan bayan dan’uwanta ya kamu da cutar, ita ma Asma an gano cewa tana dauke da cutar ta HIV.
Iyalansu sun yi amannar cewa sun samu cutar ne bayan an yi amfani da allurar da aka yi wa wasu amfani da ita, sa’ilin da suka je duba lafiya a wata asibitin gwamnati da ke garin Taunsa, a lardin Punjab na kasar Pakistan.
Suna daga cikin yara 331 da sashen binciken kwakwaf na Africa Eye ta gano cewa suna dauke da cutar HIV a birnin tsakanin watan Nuwamban 2024 zuwa Oktoban 2025.
Tun bayan da wani likita a wani asibiti mai zaman kansa ya alakanta asibitin mai suna THK Taunsa da yawaitar kamuwa da cutar a karshen shekarar 2024, gwamnatin yankin ta sha alwashin yin bincike, sannna aka dakatar da babban likitan asibitin a watan Maris na 2025.Sai dai wani bincike na BBC Eye ya gano cewa an ci gaba da yi wa fiye da mutum daya amfani da allura daya har tsawon watanni bayan batun ya tashi.
A lokacin da muka kwashe tsawon sa’o’i 32 muna daukar bidiyo a asibitin THK Taunsa ta hanyar yin badda-bami, mun gano yadda ake amfani da sirinjin allura daya wa yara da dama har sau 10, wanda akwai yiwuwar hakan ya gurbata maganin allurar.
A lokuta hudu kuma mun ga yadda aka yi amfani da ruwan magani daga kwalba daya aka yi wa yara daban-daban allura.
Ba mu da masaniya kan ko wani daga cikin yaran na dauke da cutar HIV, to amma irin hakan na da hadarin yada cutar.
“Ko da ma sun canza allurar, amma suka yi amfani da sirinji daya, sirinjin na dauke da kwayar cutar, saboda haka nan za a iya yada cutar ta sabuwar allurar,” in ji Dr Altaf Ahmed, babban masanin kananan halittu kuma daya daga cikin manyan kwararru kan cutuka masu yaduwa a Pakistan, bayan kallon bidiyon.
Duk da bayanin da aka manna a bango cewar ana amfani bin dokokin da suka dace wajen yin allura – mun dauki bidiyon ma’aikatan asibitin, ciki har da likita – suna yi wa yara allura ba tare da amfani da safar hannu ta kariya ba har sau 66, kuma wani masani ya bayyana mana cewa abin da muka gani shi ne irin ,matsalar da ake fama da ita a bangaren yin allura a fadin kasar Pakistan.
Mun kuma ga yadda wata malamar jinya ke tsoma hannu cikin kwandon sharar asibiti ba tare da safar hannu ba.
“Tana karya duk wata doka ka’idar yin allura,” in ji Ahmed. Amma a lokacin da muka nuna wa sabon shugaban asibitin Dr Kasim Buzdar, bidiyon da muka dauka, ya ki amincewa bidiyon na gaskiya ne.
Ya yi ikirarin cewar yana iya yiwuwa an dauki bidiyon ne kafin ya kama aiki ko kuma “kila an hada bidiyon ne”, sannan ya dage kai da fata cewa asibitin na da aminci ga yara.
Dr Gul Kaisrani, likita a wani asibiti mai zaman kansa a yankin, shi ne na farko da ya fara gane cewa an samu barkewar cutar HIB a yankin a karshe-karshen 2024, inda ya gano cewa akwai yara da yawa wadanda aka kai su asbintin da yake aiki suna dauke da cutar HIB.
Kusan dukkanin yara 65 zuwa 70 da ya gano cewa suna dauke da HIB sun taba zuwa neman lafiya a asibitin THK Taunsa, in ji shi.
Ya tuno cewa akwai wata mata da ta fada masa cewa an yi wa karamar yarinyata allura da sirinji daya da wata yarinya daga cikin danginsu mai dauke da HIV, sannan an yi amfani da sirinjin ga wasu yaran da yawa.
Kaisrani ya ce wani mahaifi ya taba fada masa cewa ya kalubalanci yadda ake amfani da sirinji daya ga yara da yawa a asibitin na THK Taunsa, sai dai malaman jinya ba su kula shi ba.
Sashen BBC Eye ya hada alkaluma daga shirin tantance masu cutar HIV na lardin Punjab, da asibitoci masu zaman kansu da kuma wasu alkaluma da da suka fito daga ‘yansanda wadanda suka bayyana yara 331 da aka yi wa gwaji aka gano suna dauke da cutar HIV a garin Taunsa tsakanin Nuwamban 2024 zuwa Oktoban 2025.
Daga cikin yara 97 na yaran da aka gane suna dauke da cutar HIV, wadanda kuma aka yi wa iyayensu gwaji, iyaye hud ne kacal aka samu suna dauke da cutar.
Wannan ya nuna cewa kalilan ne cikin wadannan yara suka samu cutar daga iyayensu a lokacin haihuwa.
Mahaifiyar Mohammed Amin da Asma, wato Sughra, ba ta dauke da cutar – mijinta kuma ya rasu shekara biyu da suka gabata sanadiyyar hadarin mota.
Sakamakon binciken da hukumomin lardin suka yi ya nuna cewa “sirinjin da ya gurabata da cuta” na daga cikin hanyar da fiye da rabin yara 331 suka kamu da cutar, ciki har da Asma – sauran kuma ba a bayyana hanyar da suka samu cutar ba.
Gwamnatin lardin Punjab ta shiga lamarin a watan Maris din 2025, lokacin da ta ce yawan yaran da suka kamu sun kai 106.
An salami shugaban likitocin asibitin THK Taunsa Dr Tayyab Farook Chandio, amma BBC Eye ya gano cewa ya ci gaba da aiki na tsawon wata uku a wani asibitin kauye.
Ya bayyana wa BBC Eye cewa ya dauki mataki ”nan take” bayan da aka sanar da shi game da yawan kamuwa da cutar HIV a asibitin THK Taunsa, amma ya ce ba asibitin ne sanadiyyar yaduwar cutar ba.
An maye gurbin Chandio da Buzdar, wanda ya shaida wa BBC cewa ya mayar da hankali sosai kan batun HIV bayan karbar aiki a watan Maris din 2025 kuma “ba ya lamuntar” Rashin daukar matakan kariya.
“Mun gudanar da shirye-shiryen bayar da horo ga malaman lafiya da ma’aikata a kan yadda za a dakile yaduwa da kuma kawar da cutar HIV.
Akwai kuma wani sashenmu mai muhimmanci kan kare kamuwa da cuta. An yi wa jami’an sashen horo a bangaren,” in ji shi.
Sai dai binciken BBC Eye ya gano ana gudanar da ayyukan babu kariya a watanni takwas bayan haka.
Bidiyon da muka dauka a watan Nuwamba da Disamban 2025, wanda aka dauka a tsawon makonni ya nuna yadda ake barin kwalbar magani a bude tare da sirinjin allura wadanda aka yi amfani da su a kan teburi, a maimakon a ajiye su a wurin da cut aba za ta iya shiga ba.
Yawancin yaran da muka ga ana kula da su a asibitin THK Taunsa ana yi musu allura ne ta hanyar allurer da akan sakala a cikin jijiya – wanda hakan ke kara hadarin kamuwa da cuta.
Ta hanyar tura magani kai-tsaye zuwa cikin jijiya, hakan zai bai wa kwayoyin cuta damar zille wa garkuwar jiki.
Mun kuma dauki bidiyon wata malamar jinya wadda ta dauko wani sirinji daga kasan teburi wanda yake dauke da sauran maganin da aka yi wa wani yaron na daban.
A maimakon ta jefa shi cikin kwandon shara sai ta mika wa abokiyar aikinta, wanda hakan ke nufin za a yi amfani da shi ga wani yaron na daban.
Lokacin da muka nun awa Buzdar bidiyon da muka dauka sai ya dage kai da fata cewa an dauki bidiyon ne kafin ya kama aiki ko kuma kawai an shirya bidiyon ne.
Lokacin da aka tambaye shi me zai fada wa iyayen yaran da ke zaune a yankin wadanda za su kalli bidiyon, sai ya ce “zan fada musu cewa su zo neman lafiya a asibitin THK Taunsa.
“A wata sanarwa, gwamnatin yankin ta ce “babu wata cikakkiyar shaida ta kararru” da ta “tabbatar cewa THK Taunsa ne asibitin da ya zama silar” barkewar cutar.
Sanarwar ta kara da cewa akwai wani shiri na hadin gwiwa tsakanin asusun kula da yara na UNICEF da hukumar lafiya ta duniya da kuma sashen kula da lafiya na yankin ya nuna cewa “rashin dokokin kula da asibitoci masu zaman kansu” da “amfani da jinin da ba a tantance ba” na daga cikin sila.
Sai dai wani rahoton shirin na shekarar 2025 wanda BBC ta gani game da barkewar cutar, ya gano matsaloli da dama irin wadanda BBC ta gano a binciken da ta yi a asibitin THK Taunsa.
“Akwai damuwa, musamman a bangaren kula da lafiyar yara,” in ji rahoton – yana cikin sassan da BBC ta dauko bidiyonsu.
“Babu wasu kayan da ake bukata na kula da lafiyar yara kuma ana yin allura babu daukar matakan kariya.
Ana sake amfani da kayan karin ruwa, ba a sanya lamba a kan alluran da ake sakala wa yara a jijiya sannan ana barin kayan karin ruwa da aka gama amfani da su a kan tebura.
Ba a bin dokokin tsaftace hannu – bahunan wanke hannu sun toshe sannan babu sinadaran tsaftace hannu.
A shekarar 2019, daruruwan yara a garin Ratodero na lardin Sindh ne aka gano cewa suna dauke da HIB bayan yin gwaji, kuma mafi yawansu iyayensu ba su dauke da cutar.
Likitan yara a yankin, Dr Imran Arbani ya shaida wa BBC cewa ya gano cewa da dama daga cikinsu sun ziyarci wasu asibitocin kuma an yi musu allurai da dama, “saboda haka akwai yiwuwar an saka musu cutar ne a lokacin yi musu magani”.
Ya zuwa 2021, yawan yaran yankin da ke fama da cutar HIV ya kai 1,500 – kuma har yanzu ana samun karuwar yara masu kamuwa.
Yayin da muke daukar bidiyo a asibitin Taunsa, an gano dandazon wasu da suka kamu da cutar a Karachi.
A yankin garin SITE, yaran da aka yi wa magani a asibitin Kulsoom Bai Balika, daga baya an gano suna dauke da cutar HIV.
Wani daga cikin iyalin yarinyar ya shaida wa BBC Eye cewa jami’an asibitin sun yi amfani da sirinji daya wajen yi wa yara da dama allura: “su kan cika sirinjin da magani su yi wa yaro allura, sai su sake cika sirinjin su yi wa wani yaron na daban allura”.
Shugaban likitocin asibitin Dr Mumtaz Shaikh ya fada a cikin tattaunawar da aka yi da shi cewa “kwararrun likitoci ba za su taba amfani da sirinji daya wajen yi wa yara da dama allura ba, saboda haka ba mu da irin haka a asibitocin gwamnati”.
Sai dai ministan lafiya na tarayya ya tabbatar cewa barkewar cutar da aka samu tsakanin mutum 84 ta faru ne sanadiyyar yin amfani da sirinji daya kan mutane daban-daban a asibitin.
Tsangwamar da ke tattare da cutar HIV na nufin cewa makwafta za su iya hana ‘ya’yansu wasa da Asma, abin da zai sa ta zama cikin kadaici yayin da kuma take fama da rashin lafiya, kamar yadda iyalanta suka bayyana.
Takan tambayi mahaifiyarta: “Mece ce matsalar da ke damu na?”Tsaye a kusa da kabarin dan’uwanta da ya rasu, Asma ta ce tana kewar sa.
“Yana wurin Allah a yanzu.”Ta bayyana wa BBC cewa tana yin karatu tukuru a makaranta.Ta ce “idan na girma ina so na zama likita.”















Discussion about this post