ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 100 A Sakkwato

by Abubakar Abba
4 months ago
Garkuwa

Shugaban karamar hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, Alhaji Abba Isa Sadik Achida, ya ce mazauna karamar hukumar na kara barin gidajensu a dare saboda karuwar yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

Ya ce yanayin ya zama babban damuwa ga mazauna yankin, gwamnatin jiha da ta tarayya, har ma da hukumomin tsaro sun kasa dakatar da hare-haren wanda a halin yanzu yana faruwa kusan kullum a wasu sassan karamar hukumar.

“Mutanen ba sa iya rufe idonsu biyu su yi bacci sosai,” in ji shi. Ya bayyana haka a yayin da yake magana da ‘yan jarida a Sakkwato.

ADVERTISEMENT

Shugaban karamar hukumar ya koka kan rayuka da dukiyoyin da suke salwanta sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a cikin ‘yan shekarun nan. Ya kara da cewa sama da mazauna 100 a halin yanzu suna hannun ‘yan bindiga a fadin yankin.

Ya ce dubban mutane yanzu suna zuwa garin Achida kowace yamma don su kwana, sannan su dawo idan gari ya waye.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

“Suna kwana a makarantun firamare da duk wani wuri da aka samu. Ba za a iya kwatanta irin kalubalan da suke fuskanta kullum ba,” in ji shi.

Achida ya kuma nuna damuwa kan ayyukan wasu da ake zargin masu bayar da bayanai ne ga masu kai hari, amma ya lura cewa al’ummomi sun fara tallafa wa hukumomin tsaro da bayanan sirri yayin da suka kafa kungiyoyin farar hula masu gadin garin.

Ya ce ‘yan bindiga suna toshe manyan tituna da dare, musamman a ranakun kasuwa a Achida da Goronyo.

Yayin da yake yabo wa Gwamna Ahmed Aliyu kan kokarinsa na inganta tsaro, shugaban karamar hukumar ya yi kira da a kara daukar matakan gaggawa, ciki har da kafa sansanin soja a Achida.

Haka kuma ya bukaci a kirkiro karin rassan ‘yansanda a Achida da Kwargaba da Chacho da sauran yakuna da suke cikin hadari. Ya jaddada bukatar samun isassun ma’aikata da kayan aiki.

A cewarsa, karamar hukumar ta fara gyaran tashoshin ‘yansanda ta Achida.

A martaninsa, kwamishinan ‘yansandan Jihar Sakkwato, Hayatu Hassan Shaffa, ya ce rundunar tana sane da halin da ake ciki kuma tana kara kokari wajen magance lamarin.

“Ba mu dauki wannan matsala da sauki ba. Za a tura karin ma’aikata da kayan aiki don dawo da komai yadda aka saba,” in ji shi.

Ya tabbatar da cewa ‘yansanda ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai dukkan sassan jihar sun kasance cikin aminci.

Rahotanni sun baya yadda wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Achida a ranar 17 ga Afrilu, suka kashe mutane biyu sannan suka sace wasu 23, ciki har da mata, yaro mai shekara 10 da masu tsaron gari.

Haka kuma a wani lamari, ‘yan bindiga sun kai hari garin Chacho awanni kafin aure, inda suka sace amarya, ‘yan mata masu daukar amarya da sauran mata tara.

Shugabannin al’umma sun ce Chacho ya samu rahoton kusan hare-hare 10 a cikin shekaru biyar da suka gabata, tare da kashe fiye da mazauna yanki 30.

Mazauna yankin sun bayyana Wurno a matsayin wuri mai yawan tashin hankali, inda mazauna yankin sau da yawa suke fuskantar matsaloli, yayin da karancin hanyar sadarwar waya ke jinkirta kiran neman agaji.

Sun yi kira a kafa sassanin sojoji da ‘yansanda na dindindin don magance hare-hare ‘yan bindiga.

Garkuwa
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Ko Barcelona Na Iya Lashe Gasar LaLiga A Yau?

Ko Barcelona Na Iya Lashe Gasar LaLiga A Yau?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.