ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Iran Ta Yi Wa Sansanonin Sojin Amurka 20 Mummunar Barna

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
Iran

Iran ta yi barna a cibiyoyin sojin Amurka 20 tun fara yaki tsakaninsu, kamar yadda hotuna da bidiyon tauraron dan’adam da BBC Berify ta tantance suka nuna, kuma an fahimci cewa hare-haren na da karin girma a kan yadda aka nuna a zahiri.

Iran ta rika kai wa muhimman cibiyoyi farmaki a fadin Gabas ta Tsakiya guda takwas tun a karshen watan Fabrairu, inda ta haddasa barnar miliyoyin Daloli ga na’urorin tsaron samaniya na zamani da jirgin zuba wa jiragen yaki mai a sama, da na’urorin hango jirage na rada.

Tehran ta rika kai hare-hare ne kan sansanonin sojin Amurka da kuma cibiyoyin soja na hadin gwiwa don mai da martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila a fadin Iran da Lebanon cikin wata ukun da suka wuce. Ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta ce ta kai hari kan wurare fiye da 13,000 a Iran tun fara Aikin sojin da suke kira ‘Epic Fury’.

ADVERTISEMENT

Amurka ta nemi takaita ganin hotunan tauraron dan’adam na tantance barnar yakin Iran inda ta roki Planet, wani babban kamfanin sadarwar tauraron dan’adam a kan ya sa takunkumin “sai-baba-ta-gani” kan sabbin hotunan Iran da na mafi yawan Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin ya kafa hujjar daukar matakin, yana cewa so yake yi, ya tabbatar “abokan gaba” ba su yi amfani da hotunansa “wajen kai hari ga dakarun Nato da sojojin kawance da kuma fararen hula” ba.

LABARAI MASU NASABA

Iran Za Ta Rufe Tehran A Mako Mai Zuwa Domin Jana’izar Ayatollah Ali Khamenei

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

Sashen BBC Berify ya yi amfani da hotunan tauraron dan’adam daga sauran kamfanonin sadarwar tauraron dan’adam daga sauran kasashen duniya da kuma tsofaffin hotuna daga kamfanin Planet wajen bin diddigin barnar da hare-haren Iran suka haddasa. Sansanonin na cikin kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Katar da Kuwait da Iraki da Jordan da Bahrain da kuma Oman.

Hakikanin adadin na iya fin haka, amma wasu masharhanta sun bayyana adadin sansanonin da Iran ta kai wa hari da yawan 28.

Mojtaba Khamenei, shugaban addini na Iran, ya yi kokarin fito da nasarorin sojojinsa wajen kai hare-hare a kan sansanonin Amurka.

A wata sanarwarsa ya yi ikirarin cewa Gabas ta Tsakiya ba za ta sake zama “wuri mai aminci” ga sansanonin Amurka ba.

Yayin da Fadar Shugaban Amurka ta nanata ikirarin cewa ta kusa shafe sojojin Iran daga doron kasa, masharhanta sun ce barnar da aka gani a sansanonin Amurka na nuna cewa hare-haren ramuwar gayya na Iran sun yi matukar tasiri kuma girmansu ya fi yadda jami’an Amurka suka amsa cewa an yi tun da farko.

Wani jami’in tsaron Amurka ya ki cewa uffan ga abubuwan da BBC Berify ta bankado, inda ya kafa hujja da “dalilan aikace-aikacen tsaro”.

Lalata na’urar kakkabo makamai ta THAAD

Daga cikin na’urori masu matukar muhimmanci da aka lalata akwai na’urorin zamani masu kakkabo makamai masu linzami guda uku a Al Ruwais da sansanin sojojin sama na Al Sader a Hadaddiyar Daular Larabawa da sansanin sojin sama na Muwaffak da ke Jordan.

An san Amurka na amfani da na’urorin kakkabo makamai masu linzami guda takwas ne kawai wadanda ake kira THAAD a takaice. An kera na’urorin da aka kai sansanonin soji daban-daban a fadin duniya a kan kudi kimanin Dala biliyan daya. Duk na’ura daya tana bukatar dakaru kimanin 100 domin sarrafa ta, sannan tana harba makamin kakkabo makami mai linzami duk guda daya a kan kimanin Dala miliyan 12.7.

Tsohon kwamandan rundunar tsaron Ireland, Bice-Admiral Mark Mellett, ya fada wa BBC Berify cewa na’urorin suna cikin wani ruhin harkokin tsaron yankin mai “matukar sarkakiya” wadanda ba za a iya “maye gurbinsu cikin sauri da sauki” ba.

Hare-haren Iran sun kuma yi matukar lalata jirgin zuba wa jiragen yaki mai a sama da bin diddigin abokan yaki a Sansanin sojin sama na Yarima Sultan a kasar Saudiyya, nazarin kwararru a kan hotunan tauraron dan’adam ya nuna, ga kuma lalataccen jirgin da hayaki daga ramukan da makamai suka yi kiri-kiri ana iya gani.

Jirgi guda daya da wani mai sharhi daga MAIAR ya tantance shi ne jirgin sintirin bin diddigin abokan yaki kirar E-3. Kafofin labaran Amurka sun ba da rahoton cewa yana kai wa fiye da Dala miliyan 700 kafin a maye gurbinsa.

A can wani gefen kuma, hare-haren Iran sun fada kan Sansanin sojin sama na Ali Al Salem da Sansanin Arifjan na Kuwait. masharhanta a MAIAR sun tantance rumbun ajiyar mai na karkashin kasa da aka lalata, rumfunan ajiye jiragen sama da wurin kwanan sojoji a hotunan tauraron dan’adam na sansanin, wanda aka kai masa hari a karo da dama lokacin da ake yakin.

Haka kuma a Sansanin Arifjan kamfanin ayyukan leken asirin tsaro mai suna Janes ya tantance gagarumar barna a na’urorin sadarwar tauraron dan’adam.

Sansanin sojin sama na Ali Al Salem, Kuwait

Girman barnar da aka yi wa cibiyoyin Amurka na da wahalar kimantawa, amma wani kiyasi a watan Mayu daga ma’aikatar tsaro ta Pentagon ya hada jimillar lissafin a kan Dala biliyan 29 – inda mafi yawan kudin mai yiwuwa aka kashe su wajen “gyara ko maye gurbin na’urorin” da aka lalata a yakin.

‘Yan jam’iyyar Dimokrat sun ce wannan mai yiwuwa bai kai hakikanin kudin da aka kashen ba.

Rahoton ya kuma gano cewa akalla jiragen sama 42 ciki har da jiragen yaki kirar F-15 da F35 da jirage marasa matuki kirar MK-9 Reaper da wani karamin jirgin kai hari kirar A-10, ko dai an lalata su ko kuma an yi musu illa tun cikin watan Fabrairu.

Idan aka kwatanta da na’urorin yaki masu tsada da sojojin Amurka ke amfani da su. An ba da rahoton cewa Iran na amfani da jirage marasa matuki masu arha da saukin maye gurbi wajen kai hare-hare kan wurare a fadin Gabas ta Tsakiya.

Kwararrun da suka yi magana da Sashen BBC Berify sun ce dabarun yakin da Iran ta bullo da su a tsawon lokacin yaki, ta hanyar canzawa daga fantsama ruwan makamai masu linzami da ke fada wa birane da sansanonin soji a fadin Gabas ta Tsakiya, zuwa hare-hare masu fada wa daidai inda aka nufa.

“Luguden makaman da [Iran] ta fara yi, ta tsara su ne a kan yawa—ta shirya su a kan rubdugu don kanainaye na’urorin kakkabo makamai masu linzami da na tsaron samaniya ta hanyar zubo su rututu da yawa,” cewar Dr Kelly Grieco, wata mai sharhi a cibiyar masu zurfin nazari ta Stimson Centre da ke Amurka.

“Cikin ‘yan kwanaki, amma, sai Iran ta sauya dabara zuwa luguden makamai kanana da suka fi fada wa daidai kan inda aka harba su, inda suke tattalin sauran makamai masu linzami da jirage marasa matuki don kai wa wasu wurare masu muhimmanci hari da karkata luguden wuta inda hatta kuskurewar hari da kadan, na iya haddasa gagarumar barna.”

Wani mai sharhi a MAIAR ya fada wa Sashen BBC Berify cewa dakarun sojin Amurka “ga alama zuciyarsu ta karbi laifi na gagarumin sakaci a farkon yakin” ta hanyar gaza kwashe jiragen saman da hare-haren jirage marasa matuki da makamai masu linzamin Iran za su iya fadawa yayin da Tehran ke bullo da sabbin dabaru.

Sun ce kamar a abin da ya faru a sansanin sojin sama na Yarima Sultan an kai hari cibiyar kafin kuma a sake kai harin da ya lalata jirgin saman.

Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khamenei ya lashi takobin cewa “kasashe da sassan yankin sun daina zama garkuwa ga sansanonin sojin Amurka,” ya kuma ce: “Amurka ba za ta sake samun wurin kwanciyar hankali a yankin ba (har) tana yin jamhuru da kafa sansanonin sojoji, sannan kullum za ta yi ta kara samun koma-baya daga tsohon matsayin da take kai.”

Kalamansa na zuwa ne kwanaki kalilan kafin tsagaita wutar Amurka da Iran ta sake lalacewa. A ranar Alhamis, rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai wani hari kan sansanin Amurka a yankin, bayan sabbin hare-haren da Amurka ta kai kudancin Iran.

Dr Grieco ta yi gargadin cewa idan yarjejeniyar tsagaita wutar Amurka da Iran mai tangal-tangal ta ruguje kuma yaki ya dawo danye, barnar da aka riga aka yi wa sansanonin sojin Amurka yanzu na nuna cewa cibiyoyin da ke fadin yankin Gulf na iya kasancewa cike da rauni.

“Yakin da ake yi yanzu ya lamushe rumbunan makaman tsaron Amurka da na kawayenta masu yawan gaske,” in ji ta.

“Babu hanyar maye gurbin makaman cikin sauri, abin da ke nufin duk wani sabon hari daga Iran zai gamu  da dan taki ne kawai na makaman kakkabo hare-hare da ake da su lokacin da yakin ya fara.”

“Luguden makaman da [Iran] ta fara yi, ta tsara su ne a kan yawa ta shirya su a kan rubdugu don kanainaye na’urorin kakkabo makamai masu linzami da na tsaron samaniya ta hanyar zubo su rututu da yawa,” cewar Dr Kelly Grieco, wata mai sharhi a cibiyar masu zurfin nazari ta Stimson Centre da ke Amurka.

“Cikin ‘yan kwanaki, amma, sai Iran ta sauya dabara zuwa luguden makamai kanana da suka fi fada wa daidai kan inda aka harba su, inda suke tattalin sauran makamai masu linzami da jirage marasa matuki don kai wa wasu wurare masu muhimmanci hari da karkata luguden wuta inda hatta kuskurewar hari da kadan, na iya haddasa gagarumar barna.”

Wani mai sharhi a MAIAR ya fada wa Sashen BBC Berify cewa dakarun sojin Amurka “ga alama zuciyarsu ta karbi laifi na gagarumin sakaci a farkon yakin” ta hanyar gaza kwashe jiragen saman da hare-haren jirage marasa matuki da makamai masu linzamin Iran za su iya fadawa yayin da Tehran ke bullo da sabbin dabaru.

Sun ce kamar a abin da ya faru a sansanin sojin sama na Yarima Sultan an kai hari cibiyar kafin kuma a sake kai harin da ya lalata jirgin saman.

Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khamenei ya lashi takobin cewa “kasashe da sassan yankin sun daina zama garkuwa ga sansanonin sojin Amurka,” ya kuma ce: “Amurka ba za ta sake samun wurin kwanciyar hankali a yankin ba (har) tana yin jamhuru da kafa sansanonin sojoji, sannan kullum za ta yi ta kara samun koma-baya daga tsohon matsayin da take kai.”

Kalamansa na zuwa ne kwanaki kalilan kafin tsagaita wutar Amurka da Iran ta sake lalacewa. A ranar Alhamis, rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai wani hari kan sansanin Amurka a yankin, bayan sabbin hare-haren da Amurka ta kai kudancin Iran.

Dr Grieco ta yi gargadin cewa idan yarjejeniyar tsagaita wutar Amurka da Iran mai tangal-tangal ta ruguje kuma yaki ya dawo danye, barnar da aka riga aka yi wa sansanonin sojin Amurka yanzu na nuna cewa cibiyoyin da ke fadin yankin Gulf na iya kasancewa cike da rauni.

“Yakin da ake yi yanzu ya lamushe rumbunan makaman tsaron Amurka da na kawayenta masu yawan gaske,” in ji ta.

“Babu hanyar maye gurbin makaman cikin sauri, abin da ke nufin duk wani sabon hari daga Iran zai gamu da dan taki ne kawai na makaman kakkabo hare-hare da ake da su lokacin da yakin ya fara.”

Iran
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

    Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

    Sarkin Zazzau Ya Umarci A Soke Wasu Al’adu Da Ke Kawo Wa Aure Cikas
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

MASU ALAKA

Iran Za Ta Rufe Tehran A Mako Mai Zuwa Domin Jana’izar Ayatollah Ali Khamenei
Kasashen Ketare

July 1, 2026
Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya
Kasashen Ketare

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

June 23, 2026
Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
Kasashen Ketare

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

June 22, 2026
Next Post
Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina

July 4, 2026
Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

July 4, 2026
Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

July 4, 2026
Kwankwasiyya Ta Buƙaci A Binciki Zargin Kasafin Kuɗin PFIPC

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 4, 2026
Gwamnan Katsina Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Cibiyar Gyaran Motoci Mai Amfani Da Hasken Rana

Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari

Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari

July 4, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa

July 4, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

NPA Ta Ɗaura Ɗamarar Magance Matsalolin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

July 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci