ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Matasa Ke Kara Shiga Harkar Tsaface-tsaface

by Leadership Hausa
1 year ago
Matasa

Labarai marasa dadin ji, na ci gaba da karade shafukan yada labarai na zumunta kan yadda kusan jiddan walahairan, mahukunta ke ci gaba da kama wasu matasa marasa imani, dauke da wasu sassan jikin ‘yan Adam, wadanda ake hasashen, suna aikata haka ne, da nufin aikata ayyukan asiri, musamman domin su zama masu arziki, a dare daya.

A farkon 2025, an cafke wani mai shekara 32 bisa zargin kashe wata buduwarsa’yar shekara 24, da yin aikin mai yiwa kasa hidima wato NYSC a Nicon Insurance Abuja.

  • Hukuma Ta Rufe Gidajen Gala A Jihar Kano
  • Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje

Ba jima ba kuma, ‘yansanda suka kama wasu a yankin Ogil, na karamar hukumar Okigwe a jihar Imo, da ake zargi, dauke da Kokon kan bil Adama.

ADVERTISEMENT

Duk dai a 2025, jami’an tsaro na ‘yan sa kai, a jihar Ogun, suka cafke, wani dan shekara 54, mai suna Adelani Oriyomi a makabartar da ke a yankin Kere, Obada-Oko, a garin Abeokuta, na jihar, bisa zargin yunkurin zakolo Kokon kan mamaci, daga cikin Kabari.

Wadannan sune wasu daga cikin rahotannin irin rashin imanin da aka wallafa, a wannan shekarar kadai.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

A 2024, rundunar ‘yansanda ta Abuja, sun kama wani mai suna Nuhu Ezra, a yanikin Lugbe dauke da Kokon kan mutum da Kasuwansa, inda wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa, ya ci karo da Kokon kan mutum da Kasuwan ne, a yayin da yake yin farauta a cikin Dajin Kuje.

Kazalika, duk dai a 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar Ondo, sun cafke wani mai suna Yusuf Adenoyin, a yankin Isua, na karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas dauke da Kokon kan bil Adama guda takwas.

A Jihar Oyo ma, rundunar ‘yansanda ta jihar ta kama wasu mutane biyu a yankin Amuloko da ke garin Ibadan, bisa zargin samun dauke da danyen Kokon kan wata mata , da ba a san kowacce ba.

A 2023, mutane biyar kowannen su Kotu ta yankewa hukuncin zama gidan kaso na shekaru sha biyu, bayan sun amsa laifin na tuno Kokon kan bil Adama a Kabari, bisa umarnin Bokansu da ya yi masu alkawarin mayar da su masu kudi.

Duk dai a 2023, kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Neja DSP Wasiu Abiodun, a cikin sanarwar da ya fitar a jihar ya bayyana cewa, rundunar ta cafke wasu mutane biyar bisa zargin samun su dauke da Kokon kan mutum.

Ya ce, bayan rundunar ta bincike su, suka amsa cewa, wani Bokansu su ne, ya umarce su samo Kokon kan mutum don ya hada masu asiri su zama masu kudi, inda ya kara da cewa, sai dai Bokan ya arce.

Wannan rashin imanin na irin wadannan matasan har ya kai ga ya zama tamkar sana’a a tsakaninsu, musamman suna ganin ta hanyar ciro wasu sassan jikin ‘yan Adama ne, hanya mafi sauki a gare su, domin su zama masu arziki.

Lamarin na bakin ciki, sai kara zama ruwan dare yake yi a tsakanin wasu matasan kasar.

Wannan lamarin ya tuna mana da Clifford Orji fitaccen rikakken dan kungiyar asiri da ‘yansandan jihar Legas suka kama a ranar 3 na watan Fabirairun 1999. Orji, ya yi kaurin suna wajen sace mutane, musamman mata domin aikata ayyukan asiri.

Batun cire sassan jikin ‘yan Adama domin aikata asiri a kasar nan, kusan za a iya cewa, maimakon irin wannan dabbacin ya ragu, kusan za a iya cewa, karuwa ma yake kara yi a kasar, wanda za a iya danganta karuwar lamarin kan rashin daukar hukunci na doka kan lokaci, inda har a wani lokacin a kanga irin wanda ake zargin da aikata wannan ta’asar, suna ci gaba da yawon su a cikin alumma ba tare da an hukunta su, bisa doka ba

Dole ne a sauya irin wannan halin na rashin hukunta wadanda ake zargin domin mutane na bukatar sanin, shin yaushe ne, aka kama irin wadannan mutane da ake zargin su aikta wannan rashin imanin, shin an gurfanar da su a gaban Kuliya, domin yin haka ne kawai zai tabbatar da girmama dokar kasa da fito da mutatun kasar nan da kuma daidaita al’amura.

Akwai matukar bukatar wayar da kan matasa domin a sauya tunaninsu zuwa aikata dabi’u masu kyau, musamma domin a cire masu tunanin son yi arziki a cikin gaggawa, musamman ta hanyar kirkiro da shirye-shiryen wayar masu da kai, da kuma sanya shirye-shiryen a cikin manhajar karatun zamani don a rinka ilimanatar da su, kan illar son zama masu arziki, a cikin dare daya.

Kazalika, akwai gagarumar gudunmawar da Malaman addinai da Sarakunan Garjajiya za su bayar a matsayinsu na shugabannin alumma wajen ilimantarwa da fadakarwa, musamman a tsakanin matasa kan illar son yin arziki a dare daya.

Wannan zai iya faruwa ne kawai, idan shugabanin suma sun kasance masu hali na gari.

Bugu da kari dole ne gwamnati ta samar da ababen more rayuwa da samar da kyakyawan yanayi ga ‘yan kasar, musamman duba da yadda rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasan kasar ya zama ruwan dare a kasar.

Dole ne kuma gwamnatin ta rage ci gaba da fifita bangaren masu arziki kuma dole ta sani cewa, tsare-tsaren da ta fito da su da ke shafar rayuwar manyan mutane, haka suna shafar rayuwar matsakaitan alumomin kasar.

Matasa
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Abubuwan Da Suka Ta Da Kura A Litttafin Janar Babangida

Abubuwan Da Suka Ta Da Kura A Litttafin Janar Babangida

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.