Wayar salula na daya daga cikin muhimman abubuwan ci gaban rayuwa da zamani ya zo da su, domin kuwa ta saukaka abubuwa da dama da suka shafi rayuwar Hausawa da sauran al’ummar wannan kasa baki-daya.
Tun bayan zuwan wayar salular a shekarar 2001, an samu sauye-sauye da dama da suka mamaye sassan rayuwar al’ummar wannan kasa ta fuskoki daban-daban, amma a wannan gabar, za mu yi duba ne da irin tasirin da ta yi a rayuwar Bahaushe kacokan.
Wadannan sauye-sauye kuwa, sun hada da: Bunkasa tattalin arziki da sada zumunta da karatu da soyayya da gurbata rayuwar matasa da yara kanana da kuma aikata kanana da manyan laifuka a tsakanin al’umma.
Bunkasa Tattalin Arziki
Ko shakka babu, ta fuskar yawaitar tattalin arziki da samun ayyukan yi, wayar salula ta yi matukar bayar da gudunmawa. Domin kuwa, hakan ya saukaka tsarin kasuwanci da karantarwa da tafiye-tafiye da sauran fannonin rayuwa baki-daya.
Sanin kowa ne cewa, matasanmu na Hausawa sun yi fice wajen sana’ar sayar da wayoyi na salula da gyaransu da sayar da cajoji da sauran dukkannin kayayyakin da suke da alaka da su, wannan ne ma yasa har aka ware musu kasuwanninsu daban a kusan dukkanin jihohin wannan kasa.
Sada Zumunci
Samuwar wayar salula a tsakanin al’ummar Hausawa, ta taimaka matuka wajen kara karfafa zumunci a tsakaninsu, musamman ma a irin wannan lokaci da al’amuran rayuwa da tattalin arziki suka zafafa, kusan kowa yake ta-kansa, sakamakon yadda tafiye-tafiye suka zama masu wahalar gaske, saboda tsadar man fetur.
Kamar yadda aka san al’ummar Hausawa da kokarin sada zumunci a tsakaninsu, wannan waya ta salula ta yi matukar taimaka musu a wannan zamani da ake ciki, domin kuwa, wurare dama da suka gagara zuwa sakamakon tsadar kudaden abin hawa, mutum yana daga zaune a inda yake zai dauki waya ya kira, ya sada zumunci.
Sannan kuma, babban abin ban sha’awar ma shi ne, da naira 100 ko 50 a cikin wayarka, za ka iya ya kiran wanda idan da zuwa za ka yi inda yake, akwai yiwuwar naira 100,000 ko 200,000, ba za ta ishe ka kudin mota da na abinci da kuma wanda za ka rike a hannunka, na zuwa da dawo ba.
Karatu
Wayar salula na taka muhimmiyar rawa matuka, a wajen fannin koyo da koyarwa da kuma yaduwar ilimi. Dukkanin malamai da dalibai, na matukar amfana da wayar salula a wannan zamani da muke ciki.
A wasu makarantun da dama, dalibai na amfani da wayar salula wajen taskance darasin malamansu ta hanyar nadar sauti ko bidiyo, wanda hakan zai ba su damar sake kunnawa daga baya a nutse, domin sake saurara.
Kazalika, yanzu ilimin ya yi sauki ba kamar a zamanin da ba, duk abin da malami ya koya wa dalibi, nan take zai sake fadada nasa bincike ta hanyar amfani da salula, domin fahimtar karatun yadda ya kamata.
Haka nan, su ma malaman, maimakon a da, sai malami ya yi ta neman littafi, yanzu yana daga zaune zai bude littattafai da dama ya yi bincikensa yadda ransa yake so, ya kuma fitar da abubuwan da yake son fitarwa, domin koya wa dalibansa.
Har ila yau, akwai nau’ikan ilimi da karatuttuka da ake yadawa ta hanyar wannan waya ta salula, kama daga kan karatuttukan addini da na zamani da zamantakewa da kuma wadanda suka shafi rayuwa ta yau da kullum.
Soyayya
A bangaren soyayya kuma, babu shakka wayar salula ta taimaka wajen hada auratayya tsakanin masoya da dama, ciki da wajen wannan kasa. Akwai wadanda suke ganin cewa, kusan kashi 50 cikin 100 na wadanda suke yin aure yanzu, suna haduwa ne ta hanyar wannan waya ta salula.
Akwai matasa da dama da suka yi aure a kasashen ketare, ko dai a samu namijin bai taba zuwa kasar da macen take ba, ko kuma ita macen ba ta taba zuwa kasar da namijin yake ba, amma abin sha’awa, haka za su hadu ta wannan kafa, su kulla soyayya mai karfi da za ta kai su ga yin aure.
Don haka, akwai wadanda suke ganin da ba don wannan waya ta salula ba, da ko dai ita macen ba za ta iya samun irin mijin da take so ba, ko kuma shi namijin, ba zai iya samun irin matar da ta yi daidai da shi ba.
Dalili kuwa, shi namijin ba shi da lokacin da zai rika zuwa wajen ‘yan mata daban-daban, har ya yi dace da irin wadda ra’ayinsu ya zo daya, haka nan ita ma macen, ba za ta iya bata lokacinta na fita zance da samari daban-daban ba, amma ta hanyar waya, abin ya fi zuwa da sauki, musamman saboda zaurukan sada zumunta da ake da su da dama, wadanda suka hada ‘yan mata da samari daban-daban.
Gurbata Rayuwar Matasa Da Yara Kanana
Duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan, musamman a yankunanmu na Arewacin wannan kasa, ya san irin tasirin da wayar salula ta yi, musamman wajen gurbata tarbiyyar matasa da yara kanana. Kafin zuwan wannan waya ta salula, a Arewacin Nijeriya za ka iya tara matasa 100, ba ka samu guda da ya taba ganin bidiyon da ake aikata zina ko kallon tsaraici kuru-kuru ba, haka nan su ma ‘yan mata, har a aurar da yarinya, ba ta taba sanin yadda namiji yake saduwa da ‘ya mace ba, amma yanzu sai kawai wadanda Allah ya tsare, musamman wadanda suka samu kulawar iyaye yadda ya kamata.
Shi yasa ake samun yawaitar zinace-zinace da kuma yawaitar zubar da ciki, saboda sharrin da wannan waya ta salula ta kawo da sunan ci gaba. Abin haushi da takaici shi ne, yadda yara kanana, suka san yadda idan ko da sun dauki ciki, sun san yadda za su je a zubar da shi, kuma duka ta hanyar amfani da wannan waya ta salula. A kwai da dama daga cikin yaran da sun ma fi masu aure sanin mu’amalar kwanciyar auren da sauran makamantansu.
Aikata Kanana Da Manyan Laifuka
Akwai nau’ikan ta’addanci da dama da yara kanana suke koya ta hanyar wayar salula, kama daga abin da shafi sace-sace, shaye-shaye, ayyukan daba, munanan akidu da kuma wasu munanan al’adu, wadanda ba su da alaka da rayuwar Bahaushe kwata-kwata.
Koda-yake, Bahaushe na cewa; “Idan an bi ta barawo, a bi ta ma bi sawu”, kamar yadda muka sani, wayar salula aba ce mai matukar muhimmanci, amma rashin amfani da ita ta hanyar da ta dace ne, hakan ke kawo dukkanin wadannan abubuwa da muka bayyana. Ma’ana, rashin kulawar iyaye tare da yi wa harkar rikon sakayyanar kashi ne, ya sa wadannan matasa da yara kanana suke samun kansu a ire-iren wannan hali.
Dalili kuwa shi ne, iyaye ne da kansu suke sayawa yaran nasu manyan wayoyi da sunan gata, wasu kuma suke sakarwa ‘ya’yan nasu nasu wayoyin, ba tare da bibiya ba. Wannan dalili ya sa, yara da dama sun ma fi iyayen nasu sanin lungu da sako na wayoyin, domin kuwa abubuwan da ‘ya’yan nasu sun fi su sani game da wayoyin.
Don haka, wannan kalubale ne ga iyaye da malaman addini da sauran shugabannin al’umma baki-daya. Wajibi ne a tashi tsaye, wajen kokarin kamo bakin zaren, tun kafin lokaci ya kurewa kowa. Duk mai bibiyar harkokin sada zumunta da abubuwan da suke faruwa a makarantu, musamman na boko a Arewacin wannan kasa, ya san akwai babbar matsala a gabanmu.
A bangare guda kuma, ya kamata mahukunta su dauki kwararan matakai a kan shafukanmu na sada zumunta, domin kuwa ya zama tamkar wani zaure na lalata tarbiyya da tusa munanan akidu ga yara kanana da kuma matasa. Mafi yawancin gurbacewar tarbiya da ake samu a halin yanzu, na da dangantaka da ire-iren wadannan zauruka na sada zumunta.
Bugu da kari, ayyukan ta’addanci da suka shafi yin garkuwa da mutane, fashi da makami, fyade da sauran makamantansu, kusan duk suna da alaka da wannan waya ta salula. Kafin zuwan waya, ko kadan ba a san ta’addancin yin garkuwa da mutane ba, amma zuwan wayar ya haifar da yadda za a saci mutanen da kuma yadda za a nemi kudaden fansa da sauran makamantansu.
Haka zalika, matasa da dama ta hanyar amfani da wayar ne suke koyon wannan mummunan ta’addanci, musamman ganin yadda mutane suke rungumar kaddara su biya makudan kudade, domin fansar ‘yan’uwansu da aka yi garkuwar da su. Haka ake biyan wadannan makudan kudade, kafin a saki wadanda aka sacen, ba tare da hukumomin tsaro sun iya ceto su ko kuma kama masu laifin ba.
Hakan, na nema ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma, domin kuwa a halin yanzu, an samu matar da ta yi garkuwa da kanta, don mijinta ya biya kudin fansa, ana kuma ci gaba da samun ‘ya’yan da suke yin garkuwa da kawunansu, domin iyayensu su biya kudin fansa.
Haka nan, da wannan waya ta salula ake shirya yadda za a yi fashi da makami, ‘ya’ya su yi wa iyayensu shune, yara su ma su yi wa iyayen gidansu shune, bayan an kwace kudaden daga bisani a basu tasu sallamar. Kwata-kwata, harkokin sun kasance babu amana da tausayi da kuma duba ya kamata a tsakanin wannan al’umma.
Har wa yau, batun yi wa ‘yan mata da matan aure fyade, shi ma na neman zama ruwan dare a cikin al’ummar Hausawa, duk kuma dai da wannan waya ta salula ake kulla yadda za a aiwatar da ta’addancin, ta hanyar samun bayanan sirri, kafin a afka wa wadanda ake so a afkawa.















Discussion about this post