ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

 ‘Yan Adawa Sun Sauya Sabuwar Dabarun Kifar Da Tinubu A 2027

by Yusuf Shuaibu
7 months ago
Adawa

A daidai lokacin da zabe 2027 ke kara karatowa, ‘yan adawa sun sauya sabuwar dabaru na ganin sun kifar da gwamnatin Shugaban kasa, Bola Tinubu a zabe 2027.

Jam’iyyar PDP ta ce tana kara kokarin sake hada gidauniyar cikin gida da kafa hadin kan siyasa mai fadi a matsayin wani bangare na dabarunta na zaben 2027.

  • Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
  • Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya

Mataimakin shugaban jam’iyyar na rikon kwarya a yakin kudu maso kudu, Emmanuel Ogidi, ya bayyana wannan a wata hira da kamfanin dillancin lamarai na Nijeriya (NAN), yana mai jaddada cewa jam’iyyar na ci gaba da dagewa wajen kare dimokuradiyya da sake tsara kanta a matsayin sahihin jam’iyyar adawa duk da rashin jituwa da ke ci gaba a wanzuwa a cikinta.

ADVERTISEMENT

Ogidi ya amince cewa PDP na fuskantar kananan matsaloli, amma ya jaddada cewa wadannan kalubale ba za su darkushe burinta na kare dimokiradiyya ba. Ya bayyana jam’iyyar a matsayin guda daya tilo mai ingancin adawa, kuma ya yi alkawarin cewa ba za ta ba ‘yan Nijeriya kunya ba.

A cewarsa, PDP tana sane da tsananin yanayin siyasar kasar a yanzu kuma tana da niyyar cika tsammanin ‘yan Nijeriya wadanda ke ganin jam’iyyar a matsayin tsarin dimokiradiyya.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Ogidi ya ce babban abin da PDP za ta mayar da hankali a kai wajen zabukan 2027 shi ne, kare dimokuradiyya, bunkasa hadin kan kasa da kuma ba ‘yan Nijeriya wani zabin gaskiya ga jam’iyyar da ke mulki.

Ya zargi APC da ba da fifiko ga samun nasarorin zabe fiye da ingantaccen shugabanci, yana tambaya dalilin da ya sa jam’iyyar mai mulki, kasa da shekaru biyu tana kan kujerar mulki, amma ta fi mai da hankali kan yakin neman zabe fiye da magance kalubalen shugabanci.

Jigon jam’iyyar PDP ya yi gargadin cewa lalacewar cibiyoyin dimokuradiyya na iya jefa kasar cikin rashin daidaito, yana tabbatar da cewa jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa don hana fadawa irin wannan yanayi.

Kazalika, jam’iyyar ADC, ta yi gargadi kan abin da ta bayyana a matsayin yunkurin da ake yayatawa kuma aka tsara shi domin tilasta wa ma’aikatan gwamnatin Nijeriya yin rajistar APC, ta hanyar aikin da ke gudana ta intanet da suke gudanarwa a halin yanzu.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya hannu a kai, ta bayyana hakan.

ADC ta ce ta samu rahotanni daga sassa daban-daban na kasar wanda ke ikirarin cewa ana matsa wa ma’aikatan gwamnati su yi rajista a jam’iyyar gwamnati a matsayin sharadi don samun tsaro a aiki, ci gaban sana’a, ko kuma ci gaba da samun abin dogaro da shi.

Jam’iyyar ta bayyana wannan yunkuri a matsayin abin da ya sab awa tsarin dimokuradiyya, tana gargadin cewa tilasta wa ‘yan kasa su kasance mambobi a wata jam’iyyar siyasa yana daidai da manyan take hakkin Dan’adam da kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya ya tanada.

A cewar ADC, abin da APC ke kira rajistar intanet yana kara daukar sabon salo na tilasta wa mutane shiga cikin jam’iyya ba da yardarsu ba.

ADC ta kara yin gargadi cewa ana zargin wannan aiki na iya zama barazana ga kwararrun ma’aikatan gwamnatin Nijeriya, wanda suka ce a bisa ka’ida ana tsammanin ya kasance mai zaman kansa, bisa cancanta, kuma aminci ga jiha ba ga kowanne jam’iyyar siyasa ba.

ADC ta yi kira ga hukumomi ciki har da hukumar kariya ta bayanai ta Nijeriya (NDPC) da kungiyoyin ma’aikata da kungiyoyin fararen hula da na kasa da kasa, da su sa ido sosai kan lamarin, tana gargadin cewa hakan na iya zama cin zarafi na iko da kuma yiwuwar take hakkin Dan’adam.

Adawa
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Siffofin Manzon Allah S.A.W (II)

Mece Ce Soyayyar Annabi SAW?

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.