Aƙalla mutane bakwai aka kashe bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai hari Unguwar Guru da ke ƙaramar hukumar Kankia a Jihar Katsina.
Rahotanni sun ce ’yan bindigan, kimanin 40, sun shiga ƙauyen da sanyin safiyar ranar Litinin, inda suka buɗe wa mutane wuta.
Mazauna ƙauyen sun ce sun riƙa shiga gidaje suna harbin mutane tare da ƙone wasu gidaje.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe shi ne Malam Sule na Unguwar Guru.
Harin ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu domin tsira.
An kuma ce harin ya shafi wasu ƙauyukan da ke kusa garin, ciki har da Duza a yankin Rimaye.
Mazauna ƙauyen sun ce Unguwar Guru na fuskantar hare-haren ’yan bindiga akai-akai, inda suka roƙi gwamnati da jami’an tsaro su ƙara yawan jami’ai a yankin.
Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Katsina, DSP Sadiq Aliyu, ya ce zai tabbatar da rahoton tare da yin ƙarin bayani.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ’yansanda ba su tabbatar da adadin waɗanda aka kashe ko gidajen da aka ƙone ba.














