ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Yankuna 2,000 Da Ka Iya Fuskantar Ambaliya

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago
Ruwa

Gwamnatin Tarayya ta ayyana yankuna guda 2,000 a fadin jihohi 33 da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) a matsayin wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa daban-daban. Cibiyar Ba da Gargadin Gaggawa kan Ambaliyar Ruwa ta Kasa (FEWSC) karkashin Ma’aikatar Muhalli ce ta fitar da wannan sabon hasashen a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, wanda zai fara aiki daga 27 ga watan Agusta zuwa 9 ga watan Satumbar 2026. Daga cikin wannan adadi, an rarraba al’ummomi 915 a jihohi 19 a matsayin wadanda ke cikin matsanancin hadari da suke bukatar daukar matakin kariya na gaggawa.

Rahoton ya nuna cewa ambaliyar za ta iya afkuwa ne sakamakon danyar kasa, da tsananin ruwan sama, da kwararar ruwan sama kamarda bakin kwarya, da cikar magudanan ruwa, da kuma karuwar ruwan koguna. Dangane da rarraba wuraren, akwai wasu yankuna 429 a jihohi bakwai da ke fuskantar babban hadari, yayin da yankuna 656 a jihohi 13 suke cikin masu saukin hadari. Jihohin da ke cikin matsanancin hadarin sun hada da Kogi, da Binuwai, da Rivers, da Edo, da Delta, da Cross River, da Bayelsa, da Akwa Ibom, da Abia, da Anambra, da Ebonyi, da Enugu, da Imo, da Ekiti, da Legas, da Ogun, da Ondo, da Osun, da kuma Oyo.

A bangaren Arewacin kasar kuwa, cibiyar ta bayyana jihohin Binuwai, da Kogi, da Kwara, da Neja, da Adamawa, da Taraba, da Kebbi a matsayin masu fuskantar babban hadari, inda ta lissafa garuruwa kamar Ilorin, da Jebba, da Bida, da Minna, da Mokwa, da Yola, da Numan, da Jalingo, da Wukari, da Birnin da Kebbi. A gefe guda kuma, Abuja (FCT) na cikin jerin masu fuskantar hadari mai sauki, tare da jihohin Nasarawa, da Filato, da Bauchi, da Borno, da Gombe, da Yobe, da Zamfara, da Sakkwato, Katsina, da Kano, da Kaduna, da Jigawa. Wuraren da aka sanya wa ido a Abuja sun hada da Garki, da Wuse, da Maitama, da Asokoro, da Gwarinpa, da Kubwa, da Kuje, Gwagwalada, da Lugbe, da sauransu.

ADVERTISEMENT

Daga karshe, cibiyar ta bukaci al’ummomin da ke cikin rukunin matsanancin hadari da su ci gaba da sanya ido, su tabbatar da hanyoyin ficewa don tsira, da kuma kare iyalai da muhimman kadarori. Ta bayar da tabbataccen kashedi ga mazauna yankunan da su guji zama, ko ajiye motoci, ko ajiye kayayyaki a wuraren da ambaliya ke bi, da dausayi, ko gabar koguna, da kuma magudanan ruwa da suka yi gangare.

An kuma umarci hukumomin ba da agajin gaggawa na jihohi, da jami’an muhalli, da masu sa ido a al’umma da su tsaurara lura a kewayen koguna, da rafuka, da gadoji, da madatsun ruwa, da kuma wuraren da zaizayar kasa ke shafa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ruwa
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.