Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC a jihar Osun, Najeem Salaam, ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa zai lashe zaɓen gwamnan jihar da ake gudanarwa muddin ba a tafka maguɗi ba. Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya kaɗa kuri’arsa a ranar Asabar.
Sai dai kuma a wani ɓangaren, ɗan takarar na ADC ya tayar da jijiyar wuya tare da nuna matuƙar damuwarsa kan yadda aka ƙi amincewa ko tantance wasu daga cikin wakilan jam’iyyarsa (party agents) a rumfunan zaɓe yayin tantancewa.
Najeem Salaam ya jaddada cewa babu wata fargaba a tare da shi kan gagarumar nasarar da zai samu, inda ya nuna tabbacin cewa ra’ayin al’umma ne zai yi tasiri idan har tsarin zaɓen ya kasance a bayyane kuma a cikin gaskiya da adalci ba tare da an yi masa katsalandan ba.
Wannan furuci na ɗan takarar na zuwa ne a tsaka da gudanar da zaɓen gwamnan jihar ta Osun, zaɓen da ke ci gaba da ɗaukar hankali duba da tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka da kuma yawan jama’ar da suka fito don kaɗa ƙuri’unsu.














