Gwamnatin Jihar Taraba ta raba kayan abinci da sauran kayayyakin buƙatun yau da kullum ga ’yan gudun hijira da ke samun mafaka a Ƙaramar Hukumar Ibi, domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta sakamakon ƙaura daga muhallansu.
An gudanar da rabon kayan ne ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Taraba (TSEMA), da nufin biyan buƙatun jin ƙai na gaggawa da kuma ƙarfafa tallafin da gwamnati ke bai wa al’ummomin da suka shiga halin ƙaura.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da shinkafa, da wake, da garri, da masara, da gishiri, spaghetti, da kayan ƙamshi, da tumatir, da man girki, da barguna, da tabarmi, da gidan sauro da atamfa.
Sakataren Zartarwa na TSEMA, Dakta Echuseh Audu, ta ce hukumar za ta ci gaba da tabbatar da cewa ’yan gudun hijira ba su fuskanci matsalolinsu su kaɗai ba. Ta kuma tabbatar wa waɗanda suka amfana da tallafin cewa Gwamnatin Jihar Taraba ƙarƙashin Gwamna Agbu Kefas za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin masu fama da buƙata.
Ta ce TSEMA za ta ƙara haɗin gwiwa da ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin gano tare da magance buƙatun ’yan gudun hijira a sassan jihar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ibi, Hon. Emmanuel Joshua Ubandoma, da sauran shugabannin al’umma sun halarci rabon kayan.














