Gwamnatin Jihar Katsina tana shirin gwajin lafiya ga ƴan jaridar da ke faɗin jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar Katsina, Dakta Bala Salisu Zango ya bayyana haka a yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki wadda ƙungiyar ƴan jarida (NUJ) ta ƙasa reshen Jihar Katsina ta shirya a wurin saukar baƙi na Alhayat Regency da ke Katsina.
Kwamishinan wanda ya wakilci gwamna a wajen taron ya umarci ƙungiyar NUJ kan su rubuto buƙatunsu a rubuce domin a aika wa gwamna.
Dakta Bala ya kuma yaba wa ƴan jaridar jihar bisa gudunmuwar da suke ba dawa wajen yaɗa sahihan labarai ga al’umma, inda ya ba da tabbacin cewa gwamnatin za ta ci gaba da tallafa masu a kowane lokaci.
Kwamishinan yaɗa labaran da al’adu ya kuma zayyano wasu ci gaba da aka samu a lokacin gwamnati mai ci yanzu da suka haɗa da ɗaga darajar gidajen talabijin na Jihar Katsina zuwa na zamani, samar da hasken rana a gidajen rediyon Jihar Katsina da yunƙurin kafa tashar rediyon FM a shiyyoyin Funtua da Daura da kuma Katsina.
Sai dai ya yi kira ga ƴan jaridar da ke jihar kan su tabbatar suna bin ƙa’idojin aikinsu yadda ya dace, inda ya ce yanzu haka gwamnati na nan tana tantance gidajen jaridu masu amfani da yanar gizo.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, shugaban ƴan jarida na ƙasa reshen Jihar Katsina, Kwamared Aminu Garba Ɗanɗagoro ya ce taron na da nufin a zauna a tattauna domin a gano matsalolin da suka dabaibaye ƴan jaridun jihar da kuma hanyoyin da za a bi don maganacesu.
Ya bayyana cewa sabon shugabancin ƙungiyar na shirin tantance kowace kafar sadarwa cika sharuɗɗan rajistar yin amfani da yanar gizo.
Kwamared Aminu ya kuma yaba wa gwamnatin, Malam Dikko Umar Raɗɗa bisa yadda take aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan jaridar da ke jihar.














