ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, September 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Trump: A Yayin Da Kallo Ya Koma Kasar Sin…

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Trump

Ziyarar Donald Trump zuwa kasar Sin ta ja hankalin duniya sosai saboda haduwar manyan kasashe biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, a lokacin da ake fama da rashin tabbas a huldar siyasa da tattalin arzikin duniya.

Dangantakar Amurka da Sin tana da tasiri sosai ga kasuwancin duniya, da ci gaban fasaha, da hanyoyin samar da kayayyaki, da kuma kwanciyar hankali a yankuna daban-daban. Saboda haka, gwamnatoci, da ’yan kasuwa, da sauran cibiyoyin duniya suna sa ido sosai kan wannan ziyara tare da fatan za ta samar da sakamako mai kyau bisa mutunta juna da hadin kai mai amfanar da kowa.

A shekarun baya-bayan nan, an samu karin rashin jituwa tsakanin Washington da Beijing musamman biyo bayan kare-kare harajin gwamnatin Amurka na wuce misali da kakaba takunkumai marasa kan gado a bangaren ci gaban fasaha da kuma batun Taiwan.

ADVERTISEMENT

Wadannan matsaloli sun ta’azzara rashin tabbas ga tattalin arzikin duniya, da kawo tangarda ga hanyoyin samar da kayayyaki da sauran tarnaki.

Kasashe da dama suna tsoron cewa ci gaba da rashin jituwa a tsakanin giwayen na duniya guda biyu zai iya raba hadin kan duniya zuwa bangarorin adawar siyasa da tattalin arziki, lamarin da zai rage bunkasar tattalin arziki tare da kawo barazana ga zaman lafiyar duniya.

LABARAI MASU NASABA

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

A wannan yanayi ne ake kallon ziyarar Trump a matsayin wata dama ta daidaita dangantaka da kuma sake fifita tattaunawa mai ma’ana tsakanin kasashen biyu.

Duk da cewa masana ba sa tsammanin duk matsalolin za su kau nan take, amma al’ummar duniya na fatan ganawar za ta rage zaman dar-dar tare da samar da kyakkyawar alaka mai cike da fahimtar juna.Kasuwanci da hadin gwiwar tattalin arziki suna daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran za a tattauna musamman bisa ma’aunin girmama juna, cin moriya da samun nasara ga kowane bangare.

Don haka, ’yan kasuwa da masu zuba jari a sassan duniya suna fatan kasashen biyu za su fadada damar kasuwanci, tare da karfafa hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki.

Tun da tattalin arzikin Amurka da Sin na da alaka sosai, ci gaba da rikicin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu ba kasashen biyu kadai zai cutar ba, har ma da duniya baki daya. Bisa la’akari da haka ne ma ya sa kasar Sin ta yi ta jaddada cewa babu wanda zai yi nasara a yakin tattalin arziki da cinikayya.

Har ila yau, ana sa ran wannan ziyara za ta taimaka wajen samar da dokoki masu kyau da ingantaccen tsarin kula da fasaha, da rage takunkumi kan musayar fasaha musamman a kan kayayyakin sarrafa sadarwar na’urori na semi-conductor da kirkirarriyar basira ta AI.

Gasa mai kyau na iya karfafa kirkire-kirkire, amma rikici mara iyaka na iya tarwatsa tsarin fasahar duniya baki daya.Batun Taiwan shi ma ana sa ran zai samu kulawa yayin ziyarar bisa alakarsa da muradin kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

Nasarar wannan ziyara za ta dogara sosai kan yadda kasashen biyu za su rungumi mutunta juna da hadin kai mai amfanar da kowa. Mutunta juna yana nufin fahimtar muradun juna tare da warware sabani ta hanyar tattaunawa maimakon rikici.

Ziyarar Trump a kasar Sin tana da muhimmanci ba ga Washington da Beijing kadai ba, har ma ga duniya baki daya. Babban fata shi ne kasashen biyu za su warware sabaninsu cikin hikima, su karfafa tattaunawa, tare da samar da kyakkyawar dangantaka da za ta amfani tattalin arzikin duniya, da tsaron yankuna, da kuma zaman lafiyar duniya baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Trump
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
  • Sulaiman
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu
  • Sulaiman
    Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa
Trump
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

MASU ALAKA

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
Daga Birnin Sin

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026

Next Post
Me Ya Sa Duniya Ke Fatan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

September 14, 2026
Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

September 14, 2026
Trump

Babu Dalilin Da Zai Sa Nijeriya Yin Talauci – Obasanjo

September 14, 2026
Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

September 14, 2026
Trump

Air Peace Da United Nigeria, Jirage 2 Masu Latti Sosai Watan Agusta — NCAA

September 14, 2026
Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Shugaba Xi Ya Bayyana Alkiblar Samar Da Ci Gaba Mai Inganci A Hadin Gwiwar BRICS

Shugaba Xi Ya Bayyana Alkiblar Samar Da Ci Gaba Mai Inganci A Hadin Gwiwar BRICS

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.