ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Ƴan Bindiga Sun Hana Manoman Sakkwato Zuwa Gonakinsu, Sun Ƙaƙaba Sabbin Haraji

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 months ago
Manoma

Aƙalla mazauna ƙauyuka 26 da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato sun fara tara kuɗaɗe domin biyan sabbin harajin da ƴan bindiga suka ƙaƙaba musu, bayan da suka hana su zuwa gonakinsu gabanin fara noman damina.

Mazauna yankin sun shaida cewa ƙungiyoyin ƴan bindigar sun ba su wa’adin kwanaki uku, tare da gargaɗin cewa babu wanda zai je gona har sai an biya kuɗin harajin da suka buƙata.

Daga cikin ƙauyukan da abin ya shafa akwai Garin Faji, Cina Barka, Zululu, Dan Gari, Garin Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin Ganga, Dan Kware, Garje, Dogon Faru, Son Allah, Garin Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin Labo, Zango, Kaifin Aska, Tsauna Dogo, Tudun Wada, Rambadawa, Ga Itace, Nasarawa da Garin Idi.

ADVERTISEMENT

Wani mazaunin yankin ya ce ƴan bindigar sun yi barazanar kashewa ko sace duk wanda suka kama yana noma a wannan lokacin.

“Sun ba ƙauyukan kwanaki uku. Sun ce babu wanda zai je gona har sai an biya kuɗin. Duk wanda aka kama yana noma za a kashe shi ko kuma a sace shi, kuma ba zai samu ƴanci ba sai ya biya kuɗin fansa na Naira 500,000,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya ƙara da cewa mazauna yankunan sun riga sun fara tara kuɗi domin biyan abin da aka nema.

Wani mazaunin ƙauyen Zululu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gonarsa ranar Juma’a ne lokacin da ya samu labarin wannan umarni.

“Yawanci suna neman tsakanin Naira miliyan 4 zuwa Naira miliyan 6 daga kowace al’umma. Mazauna ƙauyuka suna bayar da gudummawa gwargwadon ƙarfinsu. Wasu gidaje suna biyan Naira 1,500 ko Naira 2,000, yayin da a wasu ƙauyuka manoma ke biyan har Naira 5,000 kowannensu,” ya bayyana.

Wata majiya daga Garin Idi ta ce lokacin da ƴan bindigar suka ga ana jinkirin tara kuɗin, sai suka kai hari ƙauyen inda suka yi garkuwa da kusan mutum 20 a safiyar ranar Juma’a.

“Daga baya sun sanar da shugabannin al’umma cewa dole ne a biya Naira 600,000 kafin a saki waɗanda aka sace. An tara kuɗin kuma aka biya, wanda ya sa aka saki mutanen a ranar Juma’a,” in ji shi.

Sai dai ya ce har yanzu akwai mutum biyar da ke hannun ƴan bindigar.

“Har yanzu suna riƙe da mutum biyar. Sun ce ba za su sake su ba har sai an biya harajin. Ko bayan an yi noma ma, suna iya hana mutane girbi har sai an sake biyan wani kuɗi,” a cewarsa.

Ya kuma yi zargin cewa bayan girbi, manoma kan kasance tilas su ba ƴan bindigar wani kaso na amfanin gonarsu kafin a ba su damar ajiye amfanin a rumbunansu.

“Duk shekara bayan girbi, suna karbar wani bangare na amfanin gona daga manoma kafin su ba su damar adanawa. Wannan ya zama wata babbar matsala ga al’ummominmu,” in ji shi.

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ba ta da masaniya kan lamarin.

“Ba mu da labarin irin wannan abu. Yawanci al’ummomi ba sa kai irin waɗannan rahotanni ga hukumomin tsaro,” in ji shi.

Ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin Jihar Sakkwato bai yi nasara ba, domin saƙonnin da aka aika wa kakakin gwamnan da mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro ba su samu amsa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Manoma
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas
Manoma
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Hukumar NEPZA Ta Tabbatar Wa Da Masu Zuba Jari Goyon Bayanta

Hukumar NEPZA Ta Tabbatar Wa Da Masu Zuba Jari Goyon Bayanta

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.