ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kan Tawagar Biki, Sun Kashe Mutane 2, Sun Sace Wasu

by Abubakar Sulaiman
8 months ago
Bindiga

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari kan tawagar masu halartar bikin aure a unguwar Nagunda da ke ƙaramar hukumar Kankara a Jihar Katsina, inda suka kashe aƙalla mutum biyu tare da jikkata wasu da dama, ciki har da amaryar. Harin, wanda ya faru a daren Lahadi, ya kuma kai ga sace wasu baƙin bikin da har yanzu ba a tantance adadinsu ba, kamar yadda majiyoyi a yankin suka tabbatar.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa an shiga firgici a yankin bayan da aka ji ƙarar harbe-harbe mai yawa lokacin da maharan suka mamaye unguwar. “Har zuwa safiyar Litinin, iyalai na ci gaba da ƙoƙarin tantance adadin mutanen da aka sace,” in ji majiyar. Lamarin ya jefa al’umma cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da neman bayanai kan halin da waɗanda aka sace suke ciki.

  • Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Dalilin Sakin Mutane 70 Da Ake Zargi Da Ta’addanci
  • Hare-haren ‘Yan Bindiga: An Sake Buɗe Makarantu A Kebbi Da Kwara

Harin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Katsina ke ƙoƙarin ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya da ta ce tayi da ita da ’yan bindigar da suka tuba. Kwamishinan Tsaron Ciki da Harkokin Gida na jihar, Dokta Nasir Mu’azu, ya sha kare matakin sakin wasu mutane 70 da ake zargi da laifukan ’yan bindiga, yana mai cewa matakin na daga cikin dabarun gina amincewa domin dorewar zaman lafiya a yankunan da ke fama da rashin tsaro.

ADVERTISEMENT

Mu’azu ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar ta shafi ƙananan hukumomi sama da 15, kuma har ta haifar da sakamako, ciki har da sakin kusan mutum 1,000 da aka sace a hare-haren baya. Sai dai duk da bayanan gwamnati, harin na Kankara ya sake tayar da muhawara a tsakanin jama’a, inda wasu ke nuna damuwa cewa irin waɗannan hare-hare na iya tauye adalci ga wadanda aka zalunta da ƙarfafar aikata laifi, yayin da wasu ke jaddada cewa tattaunawa da sassauci ne kaɗai hanyar samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Bindiga
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Next Post
Hadin Gwiwa Tsakanin Canada Da Sin Zai Iya Kai Su Ga Samun Ci Gaba Cikin Zaman Lafiya Da Wadata

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.