Ƙungiyar Middle Belt Forum (MBF) ta bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga da ’yan ta’adda sun tilasta wa sama da mutane 200,000 daga Kudancin Kaduna barin muhallansu.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Luka Binniyat, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar LEADERSHIP Sunday, inda ya ce ’yan bindigar sun kuma mamaye tare da korar mazauna al’ummomi da ƙauyuka sama da 245 a yankin.
Binniyat ya ce al’ummomin da lamarin ya fi shafa sun haɗa da waɗanda ke ƙananan hukumomin Sanga, da Kachia, da Kajuru, da Chikun da Kauru, da sauran yankunan Kudancin Kaduna.
Ya ce, “Sama da mutane 200,000 daga ƙananan hukumomin Sanga, da Kachia, da Kajuru, da Chikun da Kauru ne ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka raba da muhallansu. Haka kuma, ’yan bindiga sun kwace sama da al’ummomi 245 a faɗin Kudancin Kaduna.”
Binniyat, wanda ya taɓa kasancewa Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Mutanen Kudancin Kaduna (SOKAPU), ya ce mutanen da aka raba da muhallansu sun ƙara yawan ’yan gudun hijira (IDPs) da ke fama da matsalar rashin matsuguni da sauran buƙatun jin ƙai a yankin.














