Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA) reshen Jihar Katsina kuma Kwararren Likita a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina (FTH Katsina), Dakta Mohammed Abubakar, ya yi gargaɗin cewa mutum biyu zuwa uku cikin marasa lafiya 10 da aka kwantar da su sakamakon cutar diphtheria na iya rasa rayukansu.
Dakta Abubakar ya ce asibitin na fuskantar matsin lamba sakamakon ƙaruwa da masu kamuwa da cutar, musamman yara. Ya bayyana cewa kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na cibiyar killace masu cutar sun cika, yayin da sama da kashi 80 cikin 100 na marasa lafiyar yara ne. Ya ce asibitin na karɓar marasa lafiya 20 zuwa 25 a matsakaici, kuma adadin kan kai 50 a wasu makonnin.
Ya danganta yawan mace-macen da ƙarancin wani sinadarin maganin diphtheria (antitoxin), wanda ake amfani da shi wajen dakatar da illar gubar da ƙwayar cutar ke samarwa. Ya ce maganin ya yi ƙaranci na tsawon watanni kafin a samu ɗan kaɗan ta hannun gwamnati da masu bayar da tallafi. Ya kuma bayyana giɓin rigakafin yara a matsayin ɗaya daga cikin manyan dalilan sake ɓullar cutar.
Dakta Abubakar ya yi kira ga gwamnati da ta samar da ƙarin cibiyoyin killace masu cutar tare da isassun magunguna da kayan aiki, ciki har da diphtheria antitoxin, da antibiotics, da ruwan jinya da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya. Ya ce FTH Katsina na fuskantar matsin lamba kuma ana buƙatar aƙalla cibiyoyin killace masu cutar guda uku zuwa biyar domin rage cunkoso.
Ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su garzaya asibiti idan yaro ya nuna alamomin cutar kamar ciwon maƙogaro mai ɗorewa, da zazzabi, da wahalar haɗiye abinci ko ruwa da yawan yawu. Ya jaddada cewa gano cutar da wuri, da samun magani cikin gaggawa da kammala rigakafin yara na da muhimmanci wajen rage mace-macen da cutar ke haifarwa.














