ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Tinubu Ya Jaddada Shirin Tafiyarsa Tare Da Shettima

by Sani Anwar and Sulaiman
7 months ago
Tinubu

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana mataimakinsa, Kashim Shettima a matsayin “abokin tafiya na kwarai, wajen samun ci gaba.”

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, na fatattakar ta’addanci da ‘yan bindiga, wadanda a cewarsa; ba za su amince da su ba, sannan kuma ayyukansu na ta’addanci, ya saba wa al’adu da kimar Nijeriya.

  • Manoma Da Makiyaya Sun Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Filato
  • Kotu Ta Yanke Wa Jarumar Kannywood Samha Hukuncin Ɗaurin Wata 6 A Gidan Yari

Tinubu ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake bayyana bude taron majalisar tattalin arzikin kasa, a dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata.

ADVERTISEMENT

A lokacin da yake gabatar da manyan mutane, ya kira Shettima a matsayin “Mai girma mataimakin shugaban kasa, kuma shugaban majalisar tattalin arziki na kasa, Kashim Shettima, abokin tafiya na gari,” daga nan kuma sai ya gabatar da gwamnoni, ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da suka halarci taron.

Da yake komawa kan jawabinsa, shugaban ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya sabbin yunkurin karfafa jami’an tsaro da kuma dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ya kuma bayyana shirin kaddamar da shiyyoyin injiniyoyi guda bakwai, domin bunkasa ayyukan noma.

Haka zalika, ya bayyana rashin tsaro a matsayin wani babban tabarbarewar tattalin arziki tare da jaddada bukatar hada karfi da karfe, domin shawo kan lamarin.

Da yake maraba da mahalarta taron na kwanaki biyu, shugaban ya ce; taron ya nuna aniyar ci gaban kasa baki-daya.

Da yake yin karin haske kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu, Tinubu ya ce; sauye-sauyen da ake samu ta fuskar tattalin arziki, sun taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar tare da dawo da kwarin gwiwa a idon duniya.

Ya kara da cewa, samar da ababen more rayuwa a harkokin sufuri, wutar lantarki, bunkasa harkokin sadarwa, gidaje da sauransu, sun kasance abubuwan da aka fi bai wa fifiko.

Haka zalika, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, ya yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwa a tsakanin bangarorin gwamnati guda uku, yana mai bayyana majalisar zartarwa a matsayin wani muhimmin bangare na tsara alkiblar tattalin arzikin Nijeriya, ta hanyar fahimtar juna. Sannan, ya bukaci mambobin, da su ba da fifiko wajen rage talauci da samar da ayyukan yi a tsakanin matasa.

Tinubu
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
Tinubu
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Bayani Game Da Rokon EU Ga Hukumar WTO Na Kafa Tawagar Masana Kan Matsalar Dake Tsakaninta Da Sin

Kasar Sin Ta Yi Bayani Game Da Rokon EU Ga Hukumar WTO Na Kafa Tawagar Masana Kan Matsalar Dake Tsakaninta Da Sin

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.