ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Al’ummar Karamar Hukumar Kauru Sun Nemi Ɗaukin Gwamnati Kan Barazanar Tsaro

by Shehu Yahaya and Sulaiman
5 months ago
Kauru

Al’ummar karamar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta gaggauta kawo musu dauki kan matsalar rashin tsaro da ke barazanar raba su da muhallansu.

Mazauna yankin, wadanda suka hada da Musulmai da Kirista, sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun mamaye kauyuka sama da 39, inda suka kori jama’a daga gidajensu tare da yin garkuwa da mutane fiye da dubu daya.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Rage Harajin Shigo Da Shinkafa, Motoci Da Wasu Kaya 127
  • Wasu Muhimman Abubuwa Da Ba A Sani Ba Game Da Ƙwaƙwalwa

Da yake magana a madadin al’ummar yankin, mai magana da yawun su, Rabaran Musa Hassan Shadari, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai, inda ya ce al’ummar yankin wadanda galibinsu manoma ne inda yace suna neman agajin gaggawa daga gwamnati domin ceto rayuwarsu da ta iyalansu, tare da taimaka musu su ci gaba da harkokin noma kamar yadda suka saba.

ADVERTISEMENT

Ya ce hare-haren ‘yan ta’addan sun haddasa rufe masallatai sama da 26 da kuma coci- coci sama da 65 a yankuna daban-daban.

Ya kara da cewa, al’ummar yankin sun biya kudin fansa da ya kai naira miliyan 300 domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a wasu kauyukan yankin.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Shadari, ya yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa ta hanyar girke sansanonin sojoji a yankunan da abin ya shafa, musamman a wannan lokaci da ake shirin shiga damina, domin bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin tsaro.

A nasu bangaren, wasu daga cikin mazauna yankin da suka hada da Yusuf Mathew da Ibrahim Hore, sun bayyana damuwarsu kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara, suna mai cewa rayuwarsu da dukiyoyinsu na cikin hadari.

Sun bukaci hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya a yankin tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kauru
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Kauru
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Abubakar Malami Ne Yasa Ake Tuhuma Ta, Yanzu Ga Yadda Ya Ƙare – Lamido

Abubakar Malami Ne Yasa Ake Tuhuma Ta, Yanzu Ga Yadda Ya Ƙare - Lamido

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.