Ambaliyar ruwa da guguwa mai ƙarfi sun shafi rayuwar mutane aƙalla 34,533 daga iyalai 9,845 a ƙananan hukumomi 15 na Jihar Yobe. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA) ta tabbatar da cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 303 suka jikkata sakamakon wannan iftila’i da ya auku tun daga ranar 8 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Agustan 2026.
A cikin wani sabon rahoto da Daraktan Ayyukan Ceto na YOSEMA, Dr. Muhammad Ibrahim Jalo ya gabatar, ya bayyana cewa gidaje da ɗakuna 21,363 ne suka lalace ko rugujewa, lamarin da ya raba mutane 1,120 da muhallansu tare da tilasta musu neman mafaka a wasu garuruwan ko kuma sansanonin wucin gadi.
Karamar hukumar Karasuwa ce ta fi fuskantar asara inda lamarin ya shafi mutane 3,288, sai kuma babban birnin jihar, Damaturu, wanda ambaliyar ta shafi mutane 1,554 tare da yin sanadin mutuwar mutum guda.
Hukumar ta nuna cewa yawancin asarar rayuka da raunukan da aka samu sun faru ne sakamakon rugujewar gine-ginen ƙasa da ruwa ya yi wa illa, da faɗuwar kwanukan gida, da kuma bishiyoyin da iska ta kayar da su.
Haka zalika, iftila’in ya lalata muhimman kayayyakin gwamnati, ciki har da makarantun firamare da cibiyoyin kiwon lafiya a garuruwan Bursari, da Fika, da Nguru da kuma Potiskum, wanda hakan ya kawo cikas ga samun aiyukan jin dadin al’umma a yankunan.














