Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta lashe dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 20 da aka fafata a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Bauchi da aka gudanar ranar Litinin.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC) ce ta sanar da sakamakon zaɓen a daren ranar Litinin.
Shugabar hukumar, Hajiya Jummai S. Abubakar, ta ce dukkanin ‘yan takarar APM 20 sun yi nasara kuma an tabbatar da su a matsayin shugabannin ka5nanan hukumomin jihar.
BASIEC ta ce Bappah Aliyu Mohammed ya lashe Alkaleri da ƙuri’u 107,482, yayin da Umar Mohammed Aliyu ya lashe Bauchi da ƙuri’u 125,170.
Zakka Luka Magaji kuma ya lashe Bogoro da ƙuri’u 25,282.
A sauran ƙananan hukumomin, Iliya Isah ya lashe Dambam, Ya’u Samaila Sade ya lashe Darazo, Mohammed Abubakar Jibo ya lashe Dass, yayin da Ali Babayo ya lashe Gamawa.
Sauran waɗanda suka yi nasara sun haɗa da Mohammed Idris M a Ganjuwa, Mustapha Alhaji Musa a Giade, Dankawuwa Ya’u a Itas/Gadau da Inuwa Abdullahi a Jama’are.
A zaɓen kansiloli kuwa, APM ta lashe kujeru 319 daga cikin 323 da aka fafata.
Sauran kujeru huɗu SDP, NRM, ZLP da YPP ne suka lashe su, inda kowacce jam’iyya ta samu kujera ɗaya.
Shugabar BASIEC ta ce hukumar ta gudanar da zaɓen cikin ‘yanci da bin doka, tare da tabbatar da waɗanda suka samu ƙuri’u mafi yawa a matsayin waɗanda suka yi nasara.














