Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Amsa Tambaya Game Da Ziyarar Wasu ’Yan Siyasar Japan A Haikalin Yasukuni
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayar da aka yi masa a yau Asabar 15...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayar da aka yi masa a yau Asabar 15...
A yau Asabar, kasar Sin ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da zamanantarwa mara gurbata muhalli, yayin da dokarta...
Yau ranar 15 ga watan Agusta ita ce ranar kare muhalli ta kasar Sin karo na 4, haka kuma ita ce ranar da aka fara aiwatar da "Kundin Dokokin Kare Muhalli na kasar Sin" a hukumance. A daidai wannan lokaci, bari mu duba ci gaban da Sin ta samu a wannan fanni. Bisa alkaluman da aka samar, fadin dazuzzuka ya kai kashi 25% na filayen kasar, kana yawan bishiyoyi da itatuwa da aka dasa a yankunan arewa maso yammacin kasar da arewacinta da kuma arewa maso gabashinta domin inganta muhalli ya kai kashi 40.76%. Fadin kasar da ke fama da kwararowar hamada ya takaita daga kara fadi da eka dubu 343.333 a ko wace shekara zuwa raguwa da eka dubu 666.667 a ko wace shekara. Sin ta zama kasar da ta fi saurin karuwar dazuzzuka a duniya. A yayin da kasar Sin ke samun ci gaban inganta muhallinta, hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ta wannan fanni ma tana bunkasa yadda ya kamata. A watan Yuni na 2026, a taron koli na dandalin tattaunawa kan yanayin muhalli na duniya, an gudanar da wani taron na musamman mai taken "Koyi da kwarewar Sin don inganta yanayin muhalli a gabashin Afirka", wanda ya jawo hankulan jami'ai da masana daga kasashen Afirka da yawa da kungiyoyin kasa da kasa, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kyautata muhalli da samun ci gaba mai dorewa. Mahalarta taron sun kai ga cimma matsaya daya cewa, kwarewar Sin a fannin kare muhalli tana ba da muhimmiyar ma’ana ga matakin da Afirka ke dauka na karkata zuwa hanyar samun bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba, kuma hadin gwiwar Sin da Afirka a wannan fanni na da makoma mai haske. A gefen hamada dake da nisan kimanin kilomita 70 daga Nouakchott, babban birnin Mauritania, Sin da Mauritania sun kafa "Lambun shan iska na gwaji mai amfani da fasahar Sin" mai fadin ekta 4 cikin hadin gwiwa. Masana daga cibiyar binciken muhalli da yanayin kasa ta yankin Xinjiang na Kwalejin nazarin kimiyya ta Sin sun kawo wa wannan yankin kwarewar shawo kan kwararar hamada. Ministan kare muhalli na Mauritania ya yi wa matakin da Sin ke dauka lakabin "juyin-juya-hali a bangaren kiyaye muhalli dake faruwa a yanzu." Tafkin Victoria da ke gabashin Afirka da tafkin Poyang na Sin suna fuskantar matsalolin muhalli kusan iri daya, wato kwan-gaba-kwan-bayan matsayin ruwa, da asarar mabambantan halittu da karuwar ayyukan dan Adam dake illata muhalli. Masanan Sin da Afirka suna musayar ra’ayoyi a bangarori daban-daban don magance wadannan matsaloli tare, ciki har da kyautata koguna daga dukkan fannoni da gudanar da aikin noma mai kiyaye muhalli da kayyade amfani da maganin kashe kwari da kuma amfani da makamashi mai tsabta kamar hasken rana. A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, kamfanin kasar Sin ya cimma gaggarumar nasara a bangaren samar da wutar lantarki bisa makamashi mai tsabta, injunan janareto masu samar da wutar lantarki da aka harhada a tashar samar da wutar lantarki ta Busanga na kasar sun kai karfin megawatt 240, kuma suna iya samar da wutar lantarki da yawanta ya kai KWH biliyan 1.32 mai amfani da makamashi mai tsabta a ko wace shekara, matakin da ya iya yin tsimin kwal tan dubu 447, tare da rage fitar da iskar "carbon dioxide" tan miliyan 1.1 a ko wace shekara. Sin da Afirka suna rubuta sabon tarihi wajen samun jituwa tsakanin mutum da muhalli. Ba shakka, hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren kare muhalli na da makoma mai haske.(Marubuciya: MINA)
Daga fim din "Schindler's List" zuwa "All Quiet on the Western Front", fina-finan da ke nuna adawa da yaki suna sosa zukatan jama’a. A...
Ranar 15 ga watan Agusta rana ce ta kare muhalli ta kasar Sin karo na 4. Albarkacin wannan rana Sin...
A yau Jumma'a, ma'aikatar tsaron kasa ta Sin ta bukaci Japan da ta yi waiwaye kan zaluncinta na yaki a...
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasa ta Sin, Chen Xi, ya bayyana a yau Jumma'a cewa, dakarun sojin saman...
Kasar Namibia za ta yi amfani da manufar soke haraji ta kasar Sin kan kayayyakin kasashen Afrika a matsayin wata...
Jakadan kasar Sin a Nijeriya, Yu Dunhai, ya gana da ministan kula da makamashi na kasar kuma darakta janar mai...
Ya zuwa yanzu, jimillar kudin shiga na fina-finan kasar Sin na shekara ta 2026, ciki har da sayar da tikiti...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.