Asibitin Jirgin Sojin Ruwan Sin Ya Kammala Ayyukan Kiwon Lafiya A Guinea
Asibitin Jirgin Sojin Ruwan Sin Ya Kammala Ayyukan Kiwon Lafiya A Guinea By CGTN Hausa Asibitin tafi da gidanka na jirgin sojin ruwan kasar Sin mai suna Auspicious Ark, ya bar kasar Guinea a jiya Asabar, bayan kammala ziyarar sada zumunta da ayyukan kiwon lafiya a wani bangare na shirin kiwon lafiya mai taken Mission Harmony-2026. An gudanar da bikin ban kwana ga jirgin a tashar ruwa ta Conakry. Jami’an gwamnati da na rundunar sojin Guinea da jakadan Sin a kasar da babban jami’in soji na ofishin jakadancin Sin da sauran ma’aikatan ofishin da mazauna birnin da wakilan Sinawa mazauna ketare da na kamfanonin Sin, sun halarci bikin ban kwanan. Jirgin mai gudanar da ayyukan kiwon lafiya, ya isa Conakry, babban birnin Guinea ne a ranar 3 ga wata. Yayin ziyarar, ya bayar da hidimomin lafiya ga mazauna, kuma ya yi nasarar gudanar da tiyata da dama, ciki har da na idanu da na cire manyan tsiro na hanyoyin jinni. Baya ga kula da marasa lafiya, ya kuma tura tawagar jami’an lafiya masu bayar da horo zuwa asibitin abota ta Sin da Guinea, domin musayar ilimi da gudanar da ayyukan kiwon lafiya a wani sansanin soji. Firaministan kasar Guinea, Amadou Oury Bah, ya ziyarci asibitin na tafi da gidanka tare da halartar wata liyafa da aka yi a cikinsa. Ya kuma bayyana godiya bisa ziyarar da jirgin ya kai da bayyana fatan kara hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, a karin bangarori a nan gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Asibitin Jirgin Sojin Ruwan Sin Ya Kammala Ayyukan Kiwon Lafiya A GuineaBy CGTN...



















