Binciken CGTN: Sin Tana Sake Tsara Yanayin Kasuwanci Na Lokacin Zafi Na Duniya
Daga masu yawon bude ido na kasashen waje dake tururuwa zuwa biranen Sin, zuwa “na’urorin sanyaya iska” da Sin ta kera wadanda ke samun karbuwa sosai a kasuwannin kasashen waje, kasuwanci na lokacin zafi na Sin ya sake zama abin da aka fi mayar da hankali a kai a duniya a wannan lokacin zafi da muke ciki. A cewar wani binciken da kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ta fitar, kashi 86.1% na masu bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa karuwar tattalin arzikin lokacin zafi na Sin, yana nuna yadda babbar kasuwar kasar ke karfafa tattalin arzikin duniya. Ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje da Sin ta yi, ya sanya ana “zuwa Sin a ko da yaushe” kuma ya zama wani zabi mai kyau ga masu yawon bude ido da yawa na kasashen waje. Game da hakan, kashi 95.8% na wadanda suka bayyana ra’ayoyin sun bayyana cewa, Sin tana canzawa cikin sauri daga “masana’antar duniya” zuwa “kasuwar duniya” da duniya ke amfana da ita. A halin yanzu, na’urorin sanyaya daki, da fanka da injunan yin kankara, da sauran “na’urorin sanyaya iska” da Sin ta kera suna ci gaba da samun karbuwa sosai a kasuwannin kasashen waje a wannan lokacin zafi. Game da hakan, kashi 88.2% na wadanda suka bayyana ra’ayoyin sun yi imanin cewa tattalin arzikin Sin na lokacin zafi, yana kara tabbaci da sabon kuzari a cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya da ma tattalin arzikin duniya. An fitar da wannan binciken ne a dandamalin CGTN guda biyar na harsunan Ingilishi da Sifaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci.(Safiyah Ma)



















