2027: Yadda ‘Yan Siyasa Ke Amfani Da Matasa A Bangar Siyasa
A Nijeriyar yau, daya daga cikin manyan matsalolin da suka yi tarnaki da zama kafar ungulu ga wanzuwar ingantaccen tsarin mulkin dimokuradiyya shine bangar siyasa a bisa ga yadda 'yan siyasa ke amfani da matasa wajen sarawa ko babu gaba, tsoratarwa da barazana ga abokan hamayya. Rayuwar dimbin matasa a Nijeriya ta gurbace tare da shiga mawuyacin hali a dalilin samun kan su a mummunar dabi'ar bangar siyasa da mabambantan 'yan siyasa ke amfani da su domin biyan kazamar bukatar su wadda babban laifi ne a dokar zabe. Bangar siyasa matsala ce mai zaman kan ta da ke addabar matasa a Nijeriya tare da kassara rayuwar su a bisa ga yadda suke kasa amfanar kan su ballantana su amfani wasu wanda hakan na nufin bangar siyasa babbar barazana ce ga zaman lafiya da dorewar mulkin dimokuradiyya a kasar nan. A bayyane yake cewar Nijeriya na cikin kasashen duniya da ke da mafi yawan matasa a inda sama da kashi 60 zuwa 70 suke matasa masu jini a jika 'yan kasa da shekaru 30 da ke cikin adadin akalla mutane miliyan 230 na al'ummar kasar wadanda galibi rashin aikin yi ke jefa sa su aikata ayyukan assha Rahotannin baya-bayan nan a 2025–2026, sun nuna cewar duk da raguwar kididdigar rashin aikin yi a hukumance, matsalar rashin aikin yii a tsakanin matasa a Nijeriya, matsala ce mai zaman kan ta wadda rashin magance ta ke kara jefa matasa a ayyukan da ba su dace ba, ciki har da shiga bangar siyasa. A wani rahoto a 2025 ya bayyana cewa kusan matasa miliyan 80 ne a Nijeriya suke zaman kashe wando ba su da aikin yi wanda ke wakiltar kashi 53% na jimillar matasan kasar, lamarin da ke nuna gagarumar matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama a kasar da ta fi kowace kasa yawan jama'a a Afurka. A yanayin rashin aikin yi, matasa da dama na tsunduma a sabgar bangar siyasa ba wai domin sun zaba ba sai don ba su da wani zabi don haka ya zama tamkar tilas a gare su lamarin da ke zubar da kima da darajar su a cikin al'umma. Wakilin mu ya ruwaito cewar a yayin da Nijeriya ke shirin fuskantar zaben 2027, an fara ganin alamun tashin hankali a wasu wurare da suka shafi bangar siyasa ta yadda a irin wannan lokaci, galibi matasa ne ke amfani da su wajen aiwatar da ayyukan da ke haifar da tashin- tashina da ke iya jefa su a cikin matsala. A yayin da matasa ke fama da kuncin rayuwa, wasu ‘yan siyasa da dama na amfani da wannan damar wajen jawo su a cikin sha'anin bangar siyasa ta hanyar amfani da su wajen tayar da tarzoma, haddasa rikita-rikitar siyasa ko tsoratar da abokan hamayya a yayin yekuwar neman zabe ko lokacin zabe. . Bangar siyasa ta jefa matasa cikin dabi'ar shaye-shaye, kaurwcewa karatu da amfani da miyagun makamai a yayin da 'yan siyasa suka kebe 'ya'yansu ga shiga duk wata sabgar bangar siyasa da kwamacalar siyasa. A bayyane yake yadda 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa ke taka muhimmiyar rawa wajen gurbata tarbiyar matasa a Nijeriya ta hanyar saka su a cikin bangar siyasa, kazamar hanyar da suke amfani da ita wajen kai farmaki ga abokan adawa, a wasu lokutan har da wadanda suke da matsalar rikicin cikin gida. Hasalima a bayyane yake cewar yadda ake amfani da matasa a bangar siyasa tuni ya zama abin damuwa a kasar, matsalar da a kullum gaba-gaba take kara yi ba tare da 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa sun takawa lamarin burki ba saboda su ke amfana da matasan wajen cin karen su ba babbaka. A lokutan zabe manya da matsakaitan jam'iyyun siyasa kan yi amfani da matasa a dalilin zaman banzan da suke yi suna ba su kudade kalilan domin su aikata ayyukan tashanci ta hanyar afkawa abokan hamayya a jam'iyyu daban-daban. A kan wannan masu fashin bakin lamurran yau da kullum na bayyana cewar ya zama wajibi matasa su yi wa kan su karatun- ta natsu su guji shiga harkokin bangar siyasa da duk wani nau’in tashin hankali ko rikici, domin ba abin da take haifarwa face da-na-sani. A kan wannan gagarumar matsalar, da illar ta ga zaben 2027, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda Olatunji Disu, ya gargadi matasa da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar da tashin tashina a gabanin, yayin ko bayan zabe. Ya kuma ce matasa su guji yada labaran karya, kiyayya ko tsoratar da mutane ta kafafen sada zumunta domin cimma burinsu. Disu a jawabinsa a wajen wani taro a Abuja a kwana nan ya bukaci matasa da kada su bari a dauke su aikin bangar siyasa domin tayar da hankalin 'yan siyasa, yin ayyukan daba ko daukar makamai domin biyan bukatun wani dan siyasa. Maimakon haka, shugaban 'Yan Sandan ya bukaci matasan da su shiga harkokin zabe a tsarin mulkin dimokuradiyya ta hanyar lumana da bin doka da oda, tare da kare makomarsu wadda ya ce ba tasu kadai ba ce. Bangar siyasa a kodayaushe kan gurbata rayuwar matasa tare da jefa su a cikin hadarin kamu, rauni ko ma rasa rayuwa domin a dalilin hakan dubban matasa sun halaka. Hasalima sau da yawa, 'yan siyasar da ke amfani da matasa a irin wannan yanayi ba su damu da makomar su ba, burinsu kawai shi ne cimma muradun siyasar su na dankanen lokaci. A duk lokacin zabe, kasuwar aikin yi ta daban kan bude ga matasa da ke shiga bangar siyasa domin a bayyane yake cewar 'yan siyasa da ke fafutukar lashe zabe ko ta halin kaka kan dauki matasa marasa aikin yi ko wadanda ke fama da karancin samun kudiin shiga domin yi musu ayyukan banga. Galibi abin da 'yan siyasar ke bukata daga matasan shi ne biyayya da kasancewa a cikin shiri a duk lokacin da aka bukace su aiwatar da wani al'amari na bangar siyasa wanda ake bukatar su aiwatar daidai yadda aka tsara masu. ...



















