An Kaddamar Da Wani Kwas Na Horar Da Kwararru Kan Killace Kananan Makamai Na Sin Da MDD Da Afirka
A yau Talata ne aka gudanar da bikin kaddamar da ajin horar da kwararru, kan killace kananan makamai na Sin,...
A yau Talata ne aka gudanar da bikin kaddamar da ajin horar da kwararru, kan killace kananan makamai na Sin,...
A yau Talata ne aka gudanar da bikin kaddamar da ajin horar da kwararru, kan killace kananan makamai na Sin, da MDD da kasashen nahiyar Afirka a nan birnin Beijing, horon da Sin da MDD suka yi hadin gwiwar daukar nauyin gudanarwa, ga kasashen yankin manyan tafkunan Afirka ko “Great Lakes”. Horon ya samu halartar wakilai fiye da 20, daga kasashe 5 na yankin da suka hada da na Tanzania, da Uganda, da Burundi, da Congo Kinshasa, da Ruwanda, da jami’ai daga kungiyar AU, da kungiyar tarurukan kasa da kasa ta yankin, inda za su yi bita da tattaunawa tare, kan batutuwan killace kananan makamai a cikin gida, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. Mataimaki ga ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Bin, ya bayyana a gun bikin kaddamarwar, cewa kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Afirka, wajen sa kaimi ga ayyukan killace kananan makamai a yankin, da kaddamar da hadin gwiwa a wannan fanni a tsakanin bangarori daban daban da sassan kasa da kasa, da yankin baki daya, don inganta karfin kiyaye tsaron kasashen Afirka, da neman cimma burin kawar da harbe-harben bindiga a nahiyar Afirka, da kuma neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Zainab Zhang)
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, zai halarci babban taron shugabannin kasashen Afirka, da gwamnatoci da abokan hulda dangane da...
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta...
A Watan Mayu Da safiyar yau 16 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya gudanar da...
Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fadi kasa da dala 80 kan kowace ganga a ranar Talata, sakamakon kyakkyawan...
Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Myanmar Min Aung Hlaing, a babban...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ‘yancin kai ga ɓangaren shari’a yayin da...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin ta samar da cikakken tsarin ayyukan...
Mambobi da dama na jam’iyyar APC, ciki har da wasu shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu, sun fice daga APC zuwa...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.