Tallafin Tinubu: Rijiya Ta Ba Da Ruwa Guga Ya Hana
Tallafin Tinubu: Rijiya Ta Ba Da Ruwa Guga Ya Hana
Tallafin Tinubu: Rijiya Ta Ba Da Ruwa Guga Ya Hana
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan fara yakin neman zabe a ranar 19 ga Agusta, an samu kai harehare da dama da aka danganta da 'yan siyasa masu tayar da tarzoma a Kogi, Benuwai, Kano, Inugu, Kaduna, Delta, Ribas da wasu jihohi. A wasu daga cikin abubuwan da suka faru, shugabannin jam'iyyun siyasa da magoya bayansu sun ji rauni, wanda ya haifar da damuwa game da tsaron 'yan siyasa kuma ya sa fargaba a zukatan al’umma, musamman wadanda suke son goyon bayan 'yan takararsu a fili yayin da zaben ke karatowa. A yayin da jam'iyyar da ke mulki ta APC ta yi zargin aka kai wa mambobinta da magoya bayanta farmaki, yawancin rahotannin abubuwan da suka faru sun fi mayar da hankali kan mambobi da magoya bayan jam'iyyun adawa. Yawancin hare-haren da ake zargin an kai su ne kan mambobin jam'iyyar NDC da jam'iyyar ADC da jam'iyyar PDP. Jihar Kogi A ranar 15 ga Satumba, wasu 'yan ta'addan siyasa da ake zargin ‘ya’yan jam'iyyar APC mai mulki sun hana taron da ADC ta shirya a Ejule, karamar hukumar Ofu ta Jihar Kogi, inda suka tilasta wa mambobin jam'iyya da magoya bayansu gudu don neman tsira. A cewar rahotanni, abin ya faru ne a lokacin da ake zargin masu kai hari sun harba bindigogi a sama, wanda ya haifar da firgici a tsakanin mahalarta taron da mazauna yankin. Akalla daya daga cikin mambobin ADC ya ji rauni a lokacin harin kuma aka kai shi asibiti don samun kulawar likita.Mummunan lamari ya tada sabbin damuwa kan halin tsaro a karamar hukumar Ofu, saboda akwai tarihin tashin hankali da ake yi na siyasa a yankin, musamman a lokacin zabe. Idan za a iya tunata a shekarar 2019, shugabar mata ta jam'iyyar PDP a Jihar Kogi, Salome Abuh an ruwaito cewa an kona ta har lahira a gidanta a wannan karamar hukuma a yayin zaben gwamna. Jihar Benuwai A ranar 8 ga Satumba, an kai hari ga motar yakin neman zaben shugaban kasa na NDC, Peter Obi, wanda ake zargin cewa wasu ‘yan daba sun toshe hanya a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwai, sun hana shi shiga jihar a lokacin ziyarar ta’aziyya ga Yelwata. Fiye da magoya bayan dan takarar NDC guda 10 sun ji rauni kuma an kai su asibitin koyarwa na jami'ar Jihar Benuwai da ke Makurdi, bayan wannan lamari. Yayin da jam'iyyar adawa ta zargi jami'an gwamnati da tallafa wa 'yan daba, Gwamnatin Jihar Benuwai ta musanta wannan zargi. Kusan awa 24 kacal bayan faruwar lamarin, rundunar 'yansandan Jihar Benuwai ta bayyana cewa ta kama mutum 46 da ake zargi da hannu a harin. Jihar Kano A ranar 5 ga Satumba, wasu ‘yan daba sun farmaki ‘yansanda da 'yan jarida a wurin taron jam'iyyar APC a Jihar Kano. An kai musu hari a bayan jami'ar arewa maso yamma da ke kofar Nassarawa, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa ofisinsu bayan taron. An bayar da rahoton cewa masu kai hari sun lalata motar 'yan jarida kuma sun fasa gilashin baya. APC ta gudanar da taron kungiyar goyon bayan Tinubu a filin wasa na Sani Abacha a Kano, inda ta karbi wasu shugabannin jam'iyyun adawa kafin lamarin ya faru. ...
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa jam'iyyar APC a dunƙule take A Jihar Katsina kuma ita...
Duk da fara yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa da majalisar tarayya na zaɓen 2027 bisa ga dokar zaɓe ta...
Sakamakon korafe-korafe kan yadda aka tsara tawagar yakin neman zaben jam’iyyar APC na zaben 2027, na iya haifar da tashin...
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa ƴan Nijeriya za su kori jam'iyyar APC mai mulki...
Kafin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a ranar 19 ga Agusta, hukumar zaɓe mai zaman...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.