ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Kammala Aikin Gina Gidaje 250 Na “Renewed Hope” Ya Bar Baya Da Kura A Jihar Katsina

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
3 months ago
Gidaje

Batun Kammala Aikin Gina Gidaje 250 Na “Renewed Hope” Ya Bar Baya Da Kura A Jihar Katsina

Ministan gidaje da raya birane, Muttaqa Rabe Darma, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda aikin gina gidaje 250 ƙarƙashin shirin “Renewed Hope” na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke gudana a Jihar Katsina.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar gani da ido domin duba yadda aikin ke gudana a rukunin gidajen da ke kusa da Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke Jihar Katsina.

ADVERTISEMENT

Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya ce rahoton da ya karanta a ofis ya nuna cewa an kammala gina gidaje 250 ɗin gaba ɗaya, saɓanin abin da ya gani da idonsa yayin ziyarar.

Ya ce: “An rubuta a rahoto cewa gidaje 250 ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na ‘Renewed Hope’ an kammala su gaba ɗaya a Katsina, amma da na zo nan, guda 130 ne kawai aka kammala, kamar yadda kowa ya gani.”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

A cewarsa, ya bayar da umarnin a nemo ‘yan kwangilar domin jin dalilan da suka sa ba su kammala aikin ba kamar yadda aka ƙulla yarjejeniya da su tun farko.

Ministan ya yi barazanar ɗaukar mataki a kan duk wani ɗan kwangilar da aka samu da karya alƙawari ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Ya ƙara da cewa, yarjejeniyar da aka ƙulla da ‘yan kwangilar ita ce, su kammala aikin cikin watanni shida, amma yanzu kusan shekara ɗaya da rabi kenan tun bayan bayar da aikin ba tare da an kammala shi ba.

Haka kuma, ya ce babu wani bayani a rubuce daga wajen ‘yan kwangilar dangane da jinkirin aikin.

Ministan ya bayyana cewa babu inda aka ambaci ƙarin wa’adin kwangila a cikin yarjejeniyar da aka sanya hannu tsakanin gwamnati da ‘yan kwangilar kafin a ba su aikin.

Ya ce: “Babu wani dalili da ‘yan kwangila za su bayar da zai gamsar da gwamnati kan rashin kammala aikin cikin wa’adin da aka tsara.”

Dangane da matakin da gwamnati za ta ɗauka, ministan ya ce hakan zai shafi ne kawai waɗanda ba su kammala ayyukansu ba, yayin da waɗanda suka cika sharuddan kwangila ba za a ɗauki wani mataki a kansu ba.

Gidaje
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
Gidaje
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 10, Sun Ceto Mutane 31 A Jihohin Katsina Da Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.