ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Canji Bai Tsaya A Kan Lambobi Kawai Ba Bayan Da Sin Ta Soke Haraji A Kan Kayayyakin Afirka

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 month ago
Afirka

‘Ya’yan itacen Afirka irin su avocado, tufa, lemu, da lemu mai dan daci (grapefruit) da aka shigo da su kasar Sin daga kasashen Afirka sun karu da yawa, inda avocado ya karu da kashi 130%, tufa da kashi 89.6%, lemu da kashi 27.9%, lemu mai dan daci kuma da kashi 11.9%. Har ila yau, kayayyakin ruwa da kayayyakin saka sun samu habaka da sama da kashi 10%.

Sama da kwanaki 100 ke nan da kasar Sin ta fara soke harajin fito a kan kayayyakin da ake shigowa da su daga dukkanin kasashen Afirka masu huldar diflomasiyya da ita, wadannan nasarorin da aka cimma sun nuna yadda hadin gwiwar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka ke kara inganta.A ranar 1 ga watan Mayu na wannan shekara, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar soke dukkanin harajin fito a kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen Afirka 53 da ke da dangantakar diflomasiyya da ita.

Bayan da aka fara aiwatar da wannan manufa, kayayyaki masu inganci daga kasashen Afirka sun gaggauta shiga kasuwar Sin, sakamakon yadda farashinsu ya ragu. In mun ba da misali da ridi, wanda ke kan gaba daga cikin kayayyakin da kasashen Afirka suke fitarwa zuwa kasar Sin, bayan aiwatar da manufar, harajin fito da kasar Sin ta sanya a kan ridin da yake shigowa daga Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka ya ragu daga kashi 10% zuwa sifiri, wanda hakan ya yi matukar kara fifikonsa ta fannin farashi a kasuwar kasar Sin.

ADVERTISEMENT

Lardin Shandong da ke gabar tekun gabashin Sin yana da tashoshin jiragen ruwa da yawa kamar Qingdao da Yantai wadanda ke da dimbin hanyoyin jigilar kayayyaki daga Afirka, kuma ita ce babbar tashar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka. Bayan wata daya da aka aiwatar da manufar soke haraji a kan kayayyakin Afirka, ridin da aka shigo da su daga Afirka ta bodar kwastam ta Qingdao ya karu zuwa sama da tan 80,000, wanda ya karu da kashi 50% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Baya ga ridin, tufa na Afirka ta Kudu, avocado na Kenya, lemu na Masar, da sauransu duk sun kara shigowa kasuwar Sin. In mun duba, harajin fito a kan man avocado na Kenya ya ragu daga kashi 20% zuwa 0, lamarin da ya sa wasu kamfanonin Sin suka ninka adadin shigowa da shi na shekara.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Bisa ga alkaluman da hukumar kwastam ta Sin ta samar, a watanni biyu na Mayu da Yuni bayan aiwatar da manufar, jimlar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga Afirka ta kai kudin Sin yuan 193.8 biliyan, wadda ta karu da kashi 23.5% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Wannan habaka ta sa jimilar cinikayya tsakanin bangarorin biyu a farkon rabin shekarar bana ta kai dala biliyan 203.5, wanda shi ne mafi girma a tarihi.

Tasirin manufar soke harajin bai tsaya a nan ba, musamman idan mun yi hangen nesa, yadda aka kiyaye karuwar kayayyakin da kasashen Afirka ke fitarwa zuwa kasar Sin zai jawo hankulan masu zuba jari na cikin gida da waje zuwa fannonin noma, sarrafa abinci, da sarrafa ma’adinai a kasashen Afirka kamar Najeriya.

Ta hanyar sarrafa kayayyaki a cikin gida don kara darajar kayayyakin, sannan a fitar da su zuwa kasuwar Sin, hakan zai taimaka wajen fadada tsarin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, tare da sa kaimin bunkasar fannonin nazari da kirkire-kirkiren kayayyaki da gwajin ingancin kaya da kunsa kayayyaki da ajiye kayayyaki da jigilarsu, wanda zai sa kasashen Afirka su canza daga fitar da danyun kayayyakin zuwa fitar da kayayyakin da aka sarrafa su, tare da kara karfin tattalin arzikinsu.

Kamar yadda darektan Cibiyar Nazarin Sin ta Najeriya, Charles Onunaiju ya ce, “Ba gudummawa kadai kasar Sin ta samar ba, a’a, tana taimaka wa kasashen Afirka su samu canji ta hanyar samar da kayayyaki da kasuwanci da ci gaban masana’antu.”Kwanaki 100 ba masu tsawo ba ne, amma nasarorin da aka samu ba kadan ba ne.

Jama’ar Afirka tun daga gona zuwa masana’anta, daga ma’adanan kayayyaki zuwa tashoshin jiragen ruwa suna cin moriyar “damar Sin.” Manufar soke haraji da kasar Sin ta aiwatar a kan kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Afirka masu huldar diplomasiyya da ita, ba wai rangwamen kasuwa kawai ba ne, amma misali ne da ta kafa ta fannin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. A gaba, Sin da kasashen Afirka za su ci gaba da tafiya kafada da kafada, wanda hakan zai samar da kuzari ga gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da samar da tabbas ga duniya da ke fuskantar sauye-sauye.

Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Mizanin CPI Da PPI Na Sin Ya Ci Gaba Da Hauhawa A Watan Yuli

Mizanin CPI Da PPI Na Sin Ya Ci Gaba Da Hauhawa A Watan Yuli

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.