ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Ramadan Na 13: Tsayuwar Dare

by Nuhu Ubale Ibrahim
6 months ago
Ramadan

A cikin watan Ramalana muna koyon sallar dare (Ƙiyamul-Laili), domin mu saba da tsayuwa a gaban Allah a cikin nutsuwar dare. Dare lokaci ne na sirri tsakanin bawa da Ubangijinsa; lokaci ne da hayaniyar duniya ta lafa, zukata suka natsu, kuma hawaye suka fi kusa da zubowa saboda tsoron Allah da bege gare Shi.

Tsayuwa a gaban Allah da dare tana da wani daɗi na musamman. Ba wai tsayuwar jiki kaɗai ba ce, tsayuwar zuciya ce cikin tawali’u da kaskantar da kai a wurin Allah Ta’ala. A cikin dare, mumini yana furta addu’a cikin sirri, yana neman gafara, yana roƙon rahama, yana kuma bayyana buƙatunsa ba tare da riya ko nuna wa mutane ba.

  • Darussa Daga Ramadan Na 12: Ƙarfafa Alaƙa Da Alƙur’ani A Ramalana
  • Darussa Daga Ramadan Na 11: Sauƙi Da Sassauci A Shari’a

Manzon Allah (SAW) ya bayyana girman ladan wannan ibada a cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim inda ya ce: “Duk wanda ya tsaya ya yi sallar dare a watan Ramalana yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”

ADVERTISEMENT

Mai karatu ka lura da sharaɗai biyu kamar haka:

1. Imani; watau a samu cikakkiyar yarda da cewa wannan ibada umarni ce daga Allah.
2. Neman lada; watau bawa ya yin ta domin Allah kaɗai, ba don yabo ko al’ada ba.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Idan aka haɗa waɗannan biyun, sakamakon shi ne gafara. Wace ni’ima ta fi wannan girma? Mutum ya tsaya a dare yana karanta ayoyi, yana ruku’i da sujada, sai Allah Ya shafe masa abin da ya gabata na kuskure.

Ramalana wata ne da ake raya dare da sallar Tarawihi da Tahajjud. Wannan tarbiyya ce ta ruhi. Domin duk wanda ya saba da tsayuwar dare, zuciyarsa tana samun haske, imaninsa yana ƙaruwa, kuma dangantakarsa da Allah tana ƙarfafa.

Tsayuwar dare tana koya mana:

1. Natsuwa da kame kai, domin ka bar gadonka mai daɗi ka tashi kana ganawa da Mahaliccinka.
2. Sadaukarwa; ka ba wa Allah wani ɓangare na lokacinka mafi daraja.
Sirri da ikhlasi – domin yawanci ana yin ta ne a ɓoye.
3. A haƙiƙa, tsayuwar dare alama ce ta soyayya ga Allah. Domin masoyi yana son ya kasance tare da wanda yake so, ko da a cikin dare ne.

Idan muka ɗanɗani zaƙin tsayuwar dare a Ramalana, to ya kamata mu yi ƙoƙarin ci gaba da wani kaso daga cikinta bayan Ramalana, ko da raka’a biyu ne kafin barci ko bayan tashi. Domin abin da ya fi muhimmanci shi ne dawwama, ba yawa kaɗai ba. Ramalana yana koya mana cewa gafara tana kusa da bayi, rahama tana kusa da su, yardar Allah tana kusa da su, abin da ake so shi ne; a miƙa zuciya gare Shi cikin dare.

Allah Ya sa mu kasance cikin masu tsayuwar dare da imani da neman lada, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya haskaka zukatanmu da hasken Alƙur’ani, Ya kuma sa mu zama masu kusanci da Shi a duniya da Lahira. Amin.

Ramadan
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Ramadan
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Ramadan
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Next Post
Yadda Manyan Taruka Biyu Na Sin Ke Zamowa Madubin Turbar Ci Gaban Kasar

Yadda Manyan Taruka Biyu Na Sin Ke Zamowa Madubin Turbar Ci Gaban Kasar

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.