ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Ramadan Na 5: Tsare Gaɓɓai Daga Saɓo

by Nuhu Ubale Ibrahim
5 months ago
Darussa

A cikin watan Ramalana muna koyon cewa za mu iya tsare gaɓɓanmu daga saɓon Allah domin bauta gare Shi, kamar yadda muke kame bakunanmu daga ci da sha saboda umarninsa. Idan mutum zai iya barin abin da yake so kuma yake buƙata kamar abinci da ruwan sha saboda Allah, to lallai zai iya barin saɓo saboda Allah.

Azumi ba wai yunwa da ƙishirwa kaɗai ba ne. A zahiri, yunwa da ƙishirwa horo ne ga zuciya domin ta koyi biyayya. Haƙiƙanin azumi shi ne azumin zuciya da gaɓɓai, azumin harshe daga ƙarya da gulma, azumin ido daga kallon haram, azumin kunne daga sauraron abin da bai dace ba, da azumin zuciya daga hassada da ƙiyayya. Manzon Allah (S.A.W) ya yi gargaɗi mai tsanani game da wannan ma’ana a cikin hadisin da imamul Bukhari ya ruwaito a Sahihinsa inda ya ce: “Duk wanda bai bar zuƙitamalli da aiki da ita ba, to, Allah ba Shi da buƙatar ya bar cinsa da shansa”

  • Darussa Daga Ramadan Na (3)
  • Darussa Daga Ramadan Na (4)

Wannan hadisi yana nuna cewa Allah ba Ya nufin wahalar jikin bawa kawai, amma Yana nufin gyaran hali da zuciya. Idan azumi bai hana mutum ƙarya ba, bai hana shi zalunci ba, bai hana shi gulma da cin mutunci ba, to ya rasa muhimmin ginshiƙin azumi.

ADVERTISEMENT

Ramalana makaranta ce ta horar da kai. Idan mutum zai iya kame kansa daga halal saboda Allah, to me ya sa ba zai kame kansa daga haram ba? Wannan shi ne darasin da ya kamata ya zauna a zuciya.

A zahiri, sau da yawa mutane suna kula da azumin ciki fiye da azumin gaɓɓai. Za ka ga mutum yana tsananin kiyaye bakinsa da cikinsa kada ya sha ruwa ko ya ci abinci, amma ba ya kula da abin da harshensa yake furtawa ko abin da idonsa yake kallo. Wannan kuskure ne a fahimtar azumi.

LABARAI MASU NASABA

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus

Azumi yana gina taƙawa a zuciya. Kuma taƙawa ita ce ka bar abin da Allah Ya hana ka, a fili da ɓoye. Idan azumi ya kammala zuciya da halaye, to bayan Ramalana mutum zai zama mai kiyaye dokokin Allah a sauran watanni. Saboda haka, mu sanya Ramalana ya zama wata na tsarkake gaɓɓai. Mu tsare harshenmu, mu kiyaye idanunmu, mu tsarkake zukatanmu. Mu tuna cewa Allah Yana kallon mu a kowane hali.

Allah Ya sa azuminmu ya zama azumin da ya haɗa jiki da zuciya, Ya tsare mu daga saɓo a bayyane da a ɓoye, Ya kuma sanya mu cikin bayinsa masu tsoron Sa. Amin.

Darussa
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus
Ilimi

ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus

July 3, 2026
Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa
Fatawa

Menene Hukuncin Yin Aure Da Cikin Shege?

June 21, 2026
Next Post
Wang Yi Ya Halarci Taron Manyan Jami’ai Karo Na 61 Na Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD

Wang Yi Ya Halarci Taron Manyan Jami’ai Karo Na 61 Na Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.