ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Ramadan Na 7: Farin Ciki Na Gaskiya A Rayuwar Mumini

by Nuhu Ubale Ibrahim
7 months ago
Ramadan

A cikin watan Ramalana muna koyon yadda za mu sami farin ciki da nishaɗi na gaskiya a rayuwarmu. Wannan ba farin cikin shagali ne kawai ba, ko na jin daɗin jiki kaɗai ba; a’a, farin ciki ne na ruhi da zuciya, farin cikin da yake tasowa daga jin kusanci da Allah da godiya a bisa ga tarin ni’imominsa.

Ramalana yana koya mana cewa farin ciki na gaskiya yana cikin sanin ni’ima da kuma godewa Mai bayar da ita. Duk wata ni’ima da Allah Ya yi mana, ta lafiyar jiki, da zaman lafiya, da samun iyali da arziki, da samun ikon bauta masa, to, tana buƙatar a karɓe ta da zuciyar bawa mai godiya ga Mahaliccinsa. Amma daga cikin mafi girman ni’imomi da Allah Ya yi wa bawa, akwai ni’imar shiryarwar da Allah Ya yi masa na zama a cikin addinin Musulunci; ni’imar sanin Allah, da ni’imar bin tafarkin Manzonsa (S.A.W).

  • Darussa Daga Ramadan Na 5: Tsare Gaɓɓai Daga Saɓo
  • Darussa Daga Ramadan Na (4)

Mumini yana bayyana farin cikinsa ta hanyar godewa Allah, ba ta hanyar wuce gona da iri ko mantuwa da Mai ni’ima ba. Farin cikin Musulumi yana da tushe daga imani, yana da iyaka a shari’a, kuma yana da manufa a lahira. Manzon Allah (S.A.W ) ya bayyana cewa farin cikin mai azumi ba ɗaya ba ne, biyu ne. Ya zo a cikin Sahihul Bukhari cewa ya ce: “Mai azumi yana da farin ciki biyu: yana yin farin ciki a lokacin buɗa-baki, kuma idan ya haɗu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa”

ADVERTISEMENT

Farin cikin farko, na lokacin buɗa-baki ne, farin ciki ne na halal, na jin cikar biyayya. Ba wai farin cikin cin abinci kaɗai ba ne, sai dai farin cikin kammala ibada da nasarar tsare kai daga abin da Allah Ya hana. Wannan farin ciki yana cike da ma’ana, domin yana haɗa jin daɗin jiki da nutsuwar zuciya.

Farin ciki na biyu kuwa shi ne mafi girma, farin cikin ne na haɗuwa da Allah a Lahira. Wannan shi ne farin cikin sakamakon azumi da zai samu, farin cikin lada, farin cikin ganin cewa wahalar azumi da tsare kai ba ta tafi a banza ba. Wannan farin ciki ba ya ƙarewa, ba ya gushewa, ba ya sauyawa.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Daga nan ne muke fahimtar cewa Musulmi yana rayuwa tsakanin farin ciki biyu:

1. Farin ciki na duniya wanda yake samu a cikin ibada da biyayya ga abin da Allah Ya shar’anta masa na yi ko bari.
2. Farin ciki na Lahira wanda yake jiran sakamakon aikinsa.

Ramalana yana koya mana yadda za mu daidaita farin ciki. Ba ya hana dariya ko walwala, amma yana koyar da mu cewa farin ciki na gaskiya yana cikin tsoron Allah da biyayya gare Shi. Idan zuciya ta sami nutsuwa da Allah, to ko da rayuwa ta kasance mai sauƙi ko mai wahala, mutum yana da haske a zuciyarsa.

Hakika, talauci mafi muni shi ne talaucin zuciya, kuma mafi girman wadata ita ce wadata ta imani. Wanda ya san Allah, ya ɗanɗani zaƙin ibada, ya ji daɗin azumi da salla da addu’a, to ya san cewa farin ciki ba ya cikin tara duniya kaɗai, sai dai cikin kusanci da Ubangiji.

Saboda haka, mu yi amfani da Ramalana wajen gina farin cikin ruhinmu, farin cikin da ba ya gushewa da sauyin lokaci. Mu gode wa Allah a kan ni’imar Musulunci, mu yi farin ciki da ibada, mu kuma yi fatan farin cikin haduwa da Shi a Lahira.

Allah Ya sanya mu cikin bayinsa masu farin ciki a duniya da Lahira, Ya sa mu ɗanɗani zaƙin ibada, Ya kuma ba mu farin cikin haɗuwa da Shi cikin rahama da yardarsa. Amin.

Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki

Ramadan
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Ramadan
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Ramadan
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Next Post
Jami’in Afirka Ta Kudu: Jarin Da Sin Ta Zuba Ya Ba Da Gudummarwar Samar Da Guraben Aikin Yi

Jami’in Afirka Ta Kudu: Jarin Da Sin Ta Zuba Ya Ba Da Gudummarwar Samar Da Guraben Aikin Yi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.