ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dawowar Ayyukan ‘Yan Ƙunar Baƙin Wake

by Leadership Hausa and Sulaiman
2 months ago
Bakin wake

Lokacin da ‘yan Nijeriya suka fara tunanin ko sun yi bankwana da nau’oin Bama- Baman da suka auku a shekarun baya, kamar ba za su sake aukuwa ba, sai dai ina ba’a bar garin ba sai ga kura. Litinin din da ta gabata a makon da ya wuce sai ga masu nasa Bama- Bamai da yawai sun kai hare- hare a Asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri sai kuma kasuwanni biyu, da Post Office da kuma kasuwar Mande inda suka kashe a kalla mutane 23 sai kuma 108 wadanda suka samu raunuka. Bom ya fashe ne a kofar shiga Asibitin, wato wurin da mutane suke zuwa domin neman magani can ne kuma wurin da ake rasa rayuwa.

Ga mu wadanda su ka kasance cikin lafiya, a tskanin shekarun 2011 kuma 2015, abubuwan da suka faru a Maiduguri makon da ya gabata abin da akwai zafi ya yi kuma kama da irin abubuwan da suka faru a wancan lokacin na ‘yan Boko Haram. Zuwa Coci ko Masallaci wani babban aiki ne mai wuyar tunkara. ‘Yan kasuwa mata suna yin addu’arsu kafin su fita daga gida domin sayar da Tumatir. Kare kofofin shiga zuwa wuraren addu’a sai abin ya zama an ma saba da shi ne.An rufe makarantu na makonni a lokacin. Iyaye a Arewa maso gabashin Nijeriya tsoro suke yi na aiken ‘ya’yansu zuwa wani wuri. Sannu a hankali kuma, sai Sojoji suka samu damar murkushe ‘yan Boko Haram, suka sake karbar wuraren da aka kwace masu, amma masu kai kunar Bakin Wake sun ragu. Maiduguri ta dade bata samun irin harin Bom na shekarar 2021.’Yan Nijeriya na tunanin kamar ba zai sake aukuwa ba.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamfara
  • Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta tabbatar da yawan mutanen da suka mutu. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta Jihar Borno Nahum Kenneth Dasos ya tabbatar da cewa binciken da aka yi ya nuna hare- haren da aka kai ‘yan kunar Bakin wake nr su ka kai shi. Ana ci gaba da bincike sosai, don haka za mu bar su, su yiu aikinsu.

ADVERTISEMENT

Abinda ba za ayi gardama kan shi ba shi ne irin yadda aka kai shi harin. A watan da ya wuce kadai, kungiyoyin Boko Haram da (ISWAP) sun kai hare- hare a sansanonin Sojoji da ke Jihar Borno, suka kashe a kalla Sojoji 50 da kuma yin gaba da makamai. Sojoji hamsin lalle abin ba karamin abu bane.Yawan Sojojin da suka rasa ransu ya kamata ace a ci gaba da ganin nambar a shafin farko a jaridu, amma si muka nuna abin bai dame mu ba, amma sai muka zama wasu irin mutane wajen nuna abin bai dame mu ba, kai hare- haren da ake yi sashen Arewa maso gabas, domin kuwa lamarin mutuwar Sojojin abin ya dan karade kafafen sadarwa na zamani awa 24 ne kawai, kafin mu koma maganar gulma ko gutsuri tsoma.Kasar da bata nuna alhinin mutuwar Sojojinta sosai babu wani abinda za ta iya yi wajen nuna damuwa da alhinin rasuwar Sojojinta kamar yada ya dace, babu wani abinda da za su yi wajen nuna damuwa dangane halin da tsaro yake a kasar.

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi abin,a yaba ma shi, wajen daukar matakin da ya yi da sauri. Ya nuna rashin jin dadin sa, ya kuma mika sakon ta’aziyar shi, ya umarci manyan jami’an tsaro su koma Maiduguri domin yin abinda ya dace. Dakyau haka ake bukata. Dama abinda babban kwamandan askarawan soja ya dace ya yi ke nan.Sai dai kuma mun saba da jin irin hakan. Domin Shugabannin kasa sun bada umarni ga manyan jami’an tsaro su koma wurin da lalacewar tsaro da ta’addanci abin ya fi kamari fiye da tunawar mutum. Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ma ya yi hakan lokutta masu yawa sai dai kuma duk da haka har yanzu muna kirga gawa ta wadanda aka kashe mu ke yi.Tambaya anan ita ce me ya ke faruwa ne bayan suka je wurin bayan yin kwanaki ba masu yawa ba, sai su koma Abuja. Za a ci gaba ne da maida hankali ne a wurin ko wuraren, ko amfani da dabarun asiri na Soja,ko kuma daga karshe zai kasance ne kamar yadda aka saba yi ko wane lokaci ne? ‘yan Nijeriya sun gaji da lamarin hare- hare, bakin ciki, da zama cikin zullumi, tsugunnar damu ko maida mu zuwa wani wuri, mu kasance shiru,an manta da mu har sai kuma zuwa wani lokacin da Bom ya kara tashi.

LABARAI MASU NASABA

Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan

Harin Bom ai kai shi kasa da awa 24 bayan da Sojoji sun murkushe wani harin da aka kai ma su a wajen Maiduguri. Wannan na nufin cikin kwana biyu, Birnin da aka san ramkar wata mahaifa ce ta ‘yan kungiyar Boko Haram ta fuskanci abubuwa biyu da suke da nasaba da tsaro. Hakan na iya muna mana a fili cewa akwai wani abu domin su ‘yan ta’addar ba karamin shiri suka yi ba, suna kuma da abinda ake kira da suna babu gajiya tattare da su bare wani lalaci ko yaushe a shirye suke.Har yanzu ba a samu wata babbar nasara kansu ba.Suna sake harhaduwa, samar da sabbin salon kai hare- hare domin sun gane wuraren da muke da nakasu.

Ga masu tunanin wasu abubuwa na iya faruwa ko a aiwatar da su. Kamar yadda aka sa rai ruwan sama watan Yuli a Legas, wasu mutane sun fara maganar an shirya kai hare- haren Bama- baman ne domin a kunya ta mulkin Tinubu. Ko kuma a hana shi shirin tafiyar da yake son yi zuwa hadaddiyar daular Turawa.

Kamar yadda ‘yan adawa suke kallon lamarin tafiyar ta Tinubu zuwa London kamar za ta kara ma shi tagomashi nan da zabubbukan shekara ta 2027.Na ji abubuwa masu daure kai da ban dariya a matsayi na wanda na ke kula da lamurran da suka shafi siyasar Nijeriya, amma wannan ya dace a bada nambar girmamawa ta musamman.

Irin wannan tunanin ne ya ke damuwar wadanda abin ya samu tare da iyalansu.

Maganar gaskiya ce ta dace ayi domin kuwa duk wanda yake daukar nauyin ta’addanci saboda samun wani tagomashi na siyasa ya fi su masu yin ta’addancin. Dan ta’adda wani mutum ne da wani ra’ayi ke jan hankalin shi ya yi hakan, shi kuma wanda ke daukar nauyin yana da wata manufa ta daban. Idan akwai gaskiyar da za a dogara da ita mai nuna akwai wasu ‘yan siyasa da suke kafa wadannan kungiyoyin, na kuma ji wannan magana daga wata kafa ta tsaro a shekarun da suka gabata, don haka ne ma gwamnatin Tinubu babu wata afuwa da za ta nema ayi mata akan haka, kamata ya yi ya bi ta kansu. Kar a damu da ko wanene abin ya shafa.An dade ana ta maganar wadanda suke daukar nauyin ta’addabci tun zamanin mulkin Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Bakin wake
Leadership Hausa
Website |  + posts Bio
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu
  • Leadership Hausa
    Ikirarin Cewa Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sokoto, Nauyi Ne Ga Jihar Zamfara Da Jam’iyyar APC Ba Ta Da Tushe
  • Leadership Hausa
    Nazarin Kisan Gillar Da ‘Yan Kato Da Gora Suka Yi Wa Wani Matashi A Biniwe
Bakin wake
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
  • Sulaiman
    Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
  • Sulaiman
    Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

MASU ALAKA

Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
Ra'ayinmu

Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

May 29, 2026
Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan
Labarai

Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan

May 22, 2026
Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu
Ra'ayinmu

Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu

May 15, 2026
Next Post
Kashi 60% Na Ƴan Nijeriya Ne Ke Samun Ƙasa Da ₦100,000 – Rahoto

Kashi 60% Na Ƴan Nijeriya Ne Ke Samun Ƙasa Da ₦100,000 - Rahoto

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.