ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dorewar Tattalin Arzikin Duniya Ya Dogara Ne Kan Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa Na Afrika Ta Tsakiya, Cewar Dantsoho

by Bello Hamza
3 months ago
Arzikin

Dorewa da ingantaccen fannin Tashoshin Jiragen Ruwa na Africa ta Gabas da Afirka ta Tsakiya shi ne, babban ginshikin ci gaba wanzuwar tattalin arzikin duniya.

Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Tashoshin Jiragen Ruwa na Kasa Dakta Abubakar Dantsoho ya yi wannan furucin.

Dantsoho ya bayyana haka ne, a jihar bayan kammala taron Daraktocin mahukuntan kungiyar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Africa ta Gabas da Afirka ta Tsakiya wato PMAWCA.

ADVERTISEMENT

Hukumar NPA ce, ta karbi bakuncin taron wanda ya samu halartar manyan shugabanin Hukumomin kula da Tashoshin Jiragen Ruwa da suka fito daga yankunan.

A lokacin taron, shugabanin sun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da, yadda za a kara inganta ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan da ke a yankunan da samar da kayan aiki na zamani tare da ci gaba da kara karfafa hadaka da hadin kai.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

A yayin taron, an kuma tattauna, kan yadda za a kara karfafa tsaro a tekunan da ke a yankunan da kara bunkasa hada-hadar kasuwanci da samar da kayan aiki na zamani a Tashoshin Jiragen Ruwa da ke yankunan.

Ministan kula da bunkasa fannin tattalin arziki na Teku Gboyega Oyetola, shi ma ya halarci taron.

Dantsoho a jawabinsa a wajen taron ya bayyana cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa har yanzu, su ne kan gaba wajen samar da damar gudanar da hada hadar-hadar kasuwancida kuma kara habaka fannin tattalin arzikin duniya.

Dantsoho, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ta PMAWCA ya yi nuni da cewa, daukacin shugabanin da kuma masu Ruwa da tsaki a fannin ke a yankunan akwai gudunmawar da da su taka wajen kara saita alkiblar fannin na Sufurin Jiragen Ruwa da ke a yankunan.

Ya kara da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa na ci gaba da Kasancewa hanyoyin da ke bayar da gagarumar gudunmawa wajen hada kasuwanin kasa da kasa, musamman wajen kara bunkasa fannin tattalin arziki.

Ya ci gaba da cewa, hakan na kara haifar da gudanar da shugabanci na gari tare da kuma cimma burin da aka sanya a gaba, a fannin.

Shugaban ya kuma kara jaddada cewa ci gaba da kara tumbatsar tattalin arzikin duniya, hade yake da irin kokarin da Tashoshin Jiragen Ruwa suke yi, musamman a yankuna maso tasowa da ake da bukatar kayan aiki, domin a kara bunkasa gasa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa a fadin duniya.

Shugaban ya kuma bayar da tabbacin cewa, Hukumar ta NPA, ba za ta yi kasa a guiwa, wajen ci gaba da samar da kyakyawan yanayi domin a kara ciyar da yankin gaba.

An kuma tattauna kan rahoton ayyukan kwamitin tare da kuma duba ci gaban da aka samu a tsakanin Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a yankunan.

Arzikin
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
An Yi Suka Kan Mayar Da Nijeriya Jujin Jibge Kwantaina Da Ake Shigowa Da Su

An Yi Suka Kan Mayar Da Nijeriya Jujin Jibge Kwantaina Da Ake Shigowa Da Su

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.