ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Tura Kashim Shettima Kano, Ya Yi Alƙawarin Tallafin Kuɗi Ga Ƴan Kasuwar Singa

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Mataimakin Shugabansa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Kano domin jajanta wa waɗanda gobarar Kasuwar Singer ta shafa tare da isar da saƙon tallafi. Gobarar, wadda ta tashi a daren Asabar har zuwa safiyar Lahadi, ta lalata kayayyaki da darajarsu ta kai biliyoyin naira, kuma ita ce ta biyu cikin makonni biyu a kasuwar.

A wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an ce tawagar za ta tashi daga Abuja a ranar Litinin. Za ta isar da ta’aziyyar shugaban ƙasa ga ’yan kasuwar tare da yin alƙawarin tallafin kuɗi domin sauƙaƙa musu radadin asara da kuma taimaka wa Jihar Kano wajen sake gaggauta buɗe kasuwar.

  • Ƴan Kasuwa 7 Sun ɓace, Asarar Dukiya Ta Haura Biliyan 5 A Gobarar Kasuwar Singa
  • Gobara Ta Sake Tashi A Kasuwar Singa A Kano

Mambobin tawagar sun haɗa da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; da Sanata Kawu Ismaila; da Hon. Abubakar Kabir Bichi, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai. Haka kuma, Ministan Jin-ƙai da Agajin Gaggawa, Dr. Bernard M. Doro, da Darakta-Janar na Hukumar bayar da tallafin gaggawa (NEMA), Zubaida Umar, na cikin tawagar.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce Tinubu ya riga ya tattauna ta wayar tarho da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya nuna alhini kan lamarin. Ya kuma umarci a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin maimaituwar gobarar kasuwanni domin daƙile aukuwar irin wannan a nan gaba.

Tinubu
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sin Za Ta Ba Da Damar Shiga Kasarta Ba Biza Ga ‘Yan Kanada Da Birtaniya Daga 17 Ga Fabrairu

Sin Za Ta Ba Da Damar Shiga Kasarta Ba Biza Ga 'Yan Kanada Da Birtaniya Daga 17 Ga Fabrairu

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.