ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Girke-girken Azumi (1)

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
7 months ago
Azumi

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon wanda shi ne mako kusan na karshe sai na a Azumin watan Ramadan, a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

A yau shafin na mu zai zo muku da kayatattun girke-girken Azumi:

Kamar yadda muka sani Azumi lokaci ne na girke girke da dama, kuma lokaci ne daya kamata uwargida ta tanaji abinci iri-iri, ko kuma na ce ta san mai maigida ya fi bukata lokacin buda baki da kuma lokacin Sahur, sannan lokaci ne na kirkirar abinci don burge maigida.

ADVERTISEMENT

Lokacin buda baki ana so mai Azumi ya fara buda baki da Dabino saboda sunnah ce, da shi aka ce a fara, amma ba wai dole bane, sai kayan marmari (Fruit) kamar Kankana da Lemo, Gwanda, Abarba, da dai sauransu.

Bayan wadannan ba’a so mai Azumi ya fara da ruwan sanyi, sai ki ga wasu sun fara da ruwan sanyi to gaskiya yana kawo kullewar ciki. Ana so mai Azumi ya fara da abu mai dan dumi-dumi kamar shayi ko kunu ko kuma ruwan kanwa saboda kullewar ciki ko kuma kasala da ciwon ciki dOn saboda mutum ya samu damar yin Sallar Tarawi.

LABARAI MASU NASABA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

Mene ne ruwan kanwa?

Ruwan kanwa wani ruwa ne da ake yi wa mai Azumi, yana da dadi sosai sannan idan mai Azumi ya sha ba ya sa kasala yana warware cikin mutum ko hanjin cikin mutum, idan mai Azumi ya saba da shan ruwan kanwa duk lokacin da bai sha ba ba zai taba jin dadi ba.

Ya ake ruwan kanwa?

Da farko za ki samu Gero sai a surfa shi a cire masa dusa sannan a wanke shi a shanya shi ya sha iska wato ya bushe sosai, sai ki dan soya shi ya yi kamshi, sannan ki zuba masa kayan kamshi citta, kanunfari, masoro, sai ki bayar a nika miki shi ya yi laushi sosai kamar na kunu, ki shanya shi ya bushe, sai ki ajiye shi duk idan za ki dama sai ki diba ki zuba a wani dan bokiti haka sai ki dama shi da dan ruwan kanwa dama kin dora ruwa a wuta kamar dai yadda za ki yi kunu, idan ruwa ya tafasa sai ki kashe shi ki dan barshi ya sha iska saboda kada ya zama Kunu, sai ki zuba sannan ki zuba sukari ki ajiye shi a sha shi da dumi.

Za Mu Ci GABA Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu

Azumi
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Azumi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

MASU ALAKA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
Girke-Girke

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

September 5, 2026
Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
Girke-Girke

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

August 29, 2026
Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
Girke-Girke

Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice

August 29, 2026
Next Post
Ciwon ciki

Ko Kin San...Maganin Wanke Dattin Ciki Da Mara Na Maza Da Mata?

LABARAI MASU NASABA

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.