Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dakatar da gudanar da shirin raba magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro (SMC) a faɗin jihar, biyo bayan samun rahotannin almundahana da gazawa wajen gudanar da tsarin yadda ya kamata.
Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne domin gudanar da bincike mai zurfi a kan yadda aka gudanar da rarraba magungunan da kuma yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka ware domin aikin.
Wata sanarwa da ta fito daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa an kafa kwamitin bincike na musamman wanda zai fuskanci bibiyar ma’aikata da hukumomin da ke da alhakin gudanar da tsarin.
Hukumar ta jaddada cewa ba za ta amince da kowane irin zagon ƙasa ko cin hanci da rashawa a cikin shirye-shiryen da ke da alaƙa da lafiyar al’umma ba, musamman mata da ƙananan yara.
Gwamnatin jihar ta tabbatar wa mazauna Kano cewa za ta sake dawo da shirin da zarar an kammala bincike tare da gyara duk wani kuskure domin tabbatar da magungunan sun isa ga waɗanda aka tsara dominsu.














