ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Katsina Ta Sanya Motocin Daukar Marasa Lafiya 15 A Manyan Hanyoyi

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
8 months ago
Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya sayo motocin daukar marasa lafiya guda 15 domin kula da wadanda hadari ya rutsa da su a kan manyan titunan jihar.

Da yake jawabi a lokacin karbar wadannan motocin daukar marasa lafiya, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir (ANDAJE) ya bayya cewa sayan motocin wani bangare ne na cika alkawarin da wannan gwamnatin ta yi.

  • ICPC Za Ta Ci Gaba Da Binciken Tsohon Shugaban NMDPRA Duk Da Janye Ƙarar Dangote
  • Harin Venezuela Ta’asa Ce Da Amurka Ke Tafkawa Tun Bayan Yakin Duniya Na Biyu

A cewarsa, wadannan motoci za su taimaka matuka gaya wajen ceto mutanen da suka samu hadari a manyan titunan da gwamnatin Jihar Katsina ta gyara da ma wadanda suke a gare.

ADVERTISEMENT

“A daidai lokacin da ake ta kokarin ganin an kammala manyan hanyoyin da wannan gwamnatin ke yi da kuma gyaran wadanda suka lallace, lallai akwai bukatar sanya irin wadannan motoci a kan hanya ko da an samu hadari za su taimaka sosai wajen ceton rayuka,” in ji shi.

Ya kara da cewa, Gwamna Radda ya yi alkawarin cewa zai tabbatar ya samar da harkar kiwon lafiya ingantaciya a Jihar Katsina, ya ce kawo wadannan motoci shaida ce da ke tabbatar da haka.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Hon. Abdulkadir ya ba da tabbacin cewa wadannan motoci za a doro su a kan manyan hanyoyin Jihar Katsina domin su samar da kyakkyawar yanayi na kiwon lafiya, musamman wadanda suka samu hadari suna neman taimako.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Katsina ya yi bayanin cewa gwamnan yana da wani tsari da zai kula da wadannan motoci domin dorewa da aiki da su.

Haka kuma ya ba da tabbacin cewa gwamanti za ta kafa kwamiti mai karfin gaske wanda zai hada wakilai daga hukumomin kiyaye hadura da kuma ma’aikatar lafiya ta Jihar Katsina da shugabannin kananan hukumomi domin yin aiki tare.

Ya kuma ƙara da cewa Gwamna Radda da kansa zai kaddamar da fara aikin wadannan motoci tare da rarraba su zuwa wuraren da aka tanada domin ajiye su da kuma fara aikinsu.

Katsina
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
Katsina
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Manyan Ababen More Rayuwa Ya Samu Babban Ci Gaba A 2025 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Manyan Ababen More Rayuwa Ya Samu Babban Ci Gaba A 2025 

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.