ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hajjin 2026: Alhazan Nijeriya Na Fuskantar Ƙalubalen Shiga Rawdah A Madina Saboda Matsalar Manhaja

by Sadiq
4 months ago

Mafi yawancin alhazan Nijeriya da ke shirin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026, sun tsinci kansu cikin tsaka-mai-wuya wajen samun damar shiga Rawdah da ke cikin Masallacin Manzon Allah (S.A.W) a birnin Madina.

Wannan matsala ta samo asali ne sakamakon tsarin yin rajista ta hanyar manhajar “Nusuk” wadda hukumomin Saudiyya suka samar domin tsara ziyara.

ADVERTISEMENT

An ruwaito cewa an hana wasu alhazai, musamman daga jihohin Oyo da Jigawa, shiga wannan waje mai alfarma saboda rashin yin rajista a manhajar kafin isa wajen.

Wannan yanayi ya fi shafar tsofaffi, la’akari da tsananin zafi da kuma wahalar zirga-zirga a cikin masallacin.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Wasu daga cikin maniyyatan sun bayyana cewa sun kwashe kwanaki da dama a Madina ba tare da sun samu damar shiga Rawdah ba, lamarin da ya jefa su cikin fargabar barin birnin zuwa Makkah ba tare da sun ziyarci wajen ba.

Haka kuma, sun koka kan cewa manhajar tana da sarƙaƙiya da kuma wahalar amfani.

To sai dai, wasu jami’ai sun bayyana cewa tsarin yana tafiya yadda ya kamata matuƙar an bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa.

Muhammad Aliyu, ɗaya daga cikin jami’an Amirul Hajj, ya tabbatar da cewa ya samu nasarar yin rajista ta manhajar, har ma ya taimaka wa wasu maniyyatan wajen ganin sun samu damar shiga.

A gefe guda kuma, wasu maniyyatan sun samu nasarar shiga Rawdah ta wasu ƙofofi daban bayan sun shafe lokaci suna jira, duk da cewa hakan ba ya cikin tsarin da hukuma ta amince da shi.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarancin faɗakarwa da rashin horar da maniyyata kan yadda ake amfani da sabbin fasahohi na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa wannan tsaiko.

A halin yanzu, fargaba ta mamaye zukatan maniyyata da dama kan yiwuwar barin Madina ba tare da sun gudanar da ziyara a Rawdah ba, wadda ake ɗauka ɗaya daga cikin mafi muhimmancin wurare a Musulunci.

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Manufar Cire Haraji Za Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu

Manufar Cire Haraji Za Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.