ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Uzodimma: Babu Dimokraɗiyya Idan Babu Hamayya

by Sani Anwar
3 months ago

Gwamna Hope Uzodinma, ya yi gargaɗin cewa; dimokuraɗiyyar Nijeriya, na iya fuskantar babbar barazana da haɗari, idan jam’iyyun adawa suka kasa gina manyan tsare-tsaren da za su ƙalubalanci jam’iyyar APC mai mulki, gabanin babban zaɓen 2027.

Uzodinma, ya yi magana ne a ranar Asabar a yayin zaɓen fid da gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, inda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu tikitin takara a jam’iyyar, don sake tsayawa a karo na biyu, ba tare da ƴan adawa ba.

Gwamnan na Imo ya ce, dimokuraɗiyya na samun bunƙasa ne ta hanyar hamayya, yana mai jaddada cewa; rashin samun sahihin ɗan adawa na iya raunana  dimokuraɗiyyar ƙasar.

ADVERTISEMENT

“Babu dimokuraɗiyya, idan babu ƴan adawa, ina ƙarfafa gwiwar jam’iyyun adawa da su yi aiki tuƙuru kamar yadda jam’iyya mai mulki ta yi, wanda hakan wataƙila zai iya bas u dama a nan gaba,” in ji Uzodimma.

Gwamnan ya kuma yi alfahari da cewa, nuna ƙarfi da yin abin da ya kamata na jam’iyyar APC, ya sanya jam’iyyar samun ƙarfi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Idan ka lura da abin da ke faruwa a matakin ƙasa, yadda aka zaburar da jama’a, tun daga batun yin rajistar shiga jam’iyya, wanda aka yi ta hanyar na’urar intanet, har zuwa tabbatar da mambobin ƙungiyar, za ka ga yadda kimanin mutum 35,000 a kowace mazaɓa guda a dukkanin ƙananan hukumomi suka yi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Hakan na nufin, idan dukkan ƴan jam’iyyarmu suka zaɓi shugaba Bola Tinubu, ya riga ya lashe zaɓen”.

Uzodimma ya danganta yawan fitowar jama’a da aka samu a lokacin zaɓukan fid da gwani na jam’iyyar APC da abin da ya bayyana a matsayin hada-hadar jama’a da gangan da aka ɓullo da ita ta hanyar yin rajistar shiga jam’iyyar ta dijital.

Gwamnan ya ƙara yaba wa salon jagorancin Tinubu, inda ya jaddada cewa; shugaban ƙasa ya yi abin da ya dace da ya cancanci a sake zaɓarsa a karagar mulki.

“Shugaba Bola Tinubu, ya yi abin da ya dace ya sake komawa a karo na biyu, ina so in taya shi murna da ya ɗauki lokaci ya yi siyasa yadda ya kamata,” in ji Uzodimma.

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.