ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

IAR Ta Fara Horas Da Malaman Gona Don Fuskantar Daminar Bana

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago

Cibiyar Binciken Noma ta (Institute for Agricultural Research), tare da haɗin gwiwar African Agricultural Technology Foundation da shirin BMSS, sun samu nasarar fara horarwar manoma kafin kakar noma ta shekarar 2026 domin ƙarfafa noman masara da inganta ɗorewar ayyukan noma a faɗin Nijeriya.

Shirin horarwar na kwanaki biyu, wanda ya fara ranar Talata, 12 ga Mayun 2026, ya haɗa mahalarta daga jihohi daban-daban na ƙasar, ciki har da manoma, masu bincike, jami’an yaɗa harkokin noma da ƙwararrun masu fasaha, waɗanda suka duƙufa wajen inganta yawan amfanin masara ta hanyar amfani da dabarun noma na zamani da kuma hanyoyin yaƙi da ƙwari masu lalata amfanin gona.

An fara shirin da addu’o’i da gabatar da kai, lamarin da ya bai wa mahalarta damar mu’amala, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar noman masara.

ADVERTISEMENT

A jawabin maraba, babban mai bincike na shirin BMSS, Farfesa Rabiu S. Adamu, ya nuna godiya bisa yadda mahalarta suka amsa gayyata duk da ɗan ƙanƙanin lokacin sanarwa kafin fara shirin.

Ya jaddada cewa an tsara horarwar ne domin ƙarfafa noman masara, musamman a Arewacin Nijeriya, ta hanyar ingantattun dabarun noma, kula da ƙwari da cututtukan amfanin gona yadda ya kamata, da kuma amfani da ingantattun hanyoyin kula da Tela Maize.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Babban Daraktan Institute for Agricultural Research, Farfesa Ado Yusuf, wanda Mataimakin Daraktan Bincike, Farfesa L. J. Bamaiyi ya wakilta, ya bayyana horarwar a matsayin wacce ta zo a kan lokaci kuma mai muhimmanci, musamman yayin da manoma da masu ruwa da tsaki a harkar noma ke shirin tunkarar kakar noman shekarar 2026.

Ya ƙarfafa mahalarta taron da su shiga cikin zaman horarwar sosai tare da amfani da damar wajen samun ilimi na aikace da na kimiyya wanda zai taimaka wajen inganta dasa amfanin gona da yawan amfanin da ake samu.

Taron ya ƙunshi gabatar da muhimman muƙaloli daga fitattun masana kimiyya da ƙwararru a fannin noman masara da kula da amfanin gona.

Farfesa Rabiu S. Adamu ya gabatar da muƙala mai taken “Kula da Muhimman Ƙwari da Cututtukan Masara,” inda aka wayar da kan mahalarta kan yadda ake gano manyan ƙwari da cututtukan da ke shafar noman masara, hanyoyin kariya da yadda ake magance su.

Wata muhimmiyar muƙala da Farfesa M. M. Abdulmalik ya gabatar mai taken “Fari da Tasirinsa ga Yawan Amfanin Masara.”

Muƙalar ta mayar da hankali ne kan yadda fari ke shafar bunƙasar masara da kuma hanyoyin da manoma za su iya amfani da su wajen rage asarar amfanin gona sakamakon sauyin yanayi.

Haka kuma mahalarta sun sami ƙarin haske kan yadda ake samar da irin masara mai haɗaɗɗen jinsi (hybrid) ta hanyar gabatarwar Dakta H. Abubakar mai taken “Samar da Irin Masara na Hybrid.”

Muƙalar fasaha ta ƙarshe ta ranar kuwa Dakta M. S. Usman ne ya gabatar mai taken “Kula da Juriyar Ƙwari a Tsarin Kula da Tela Maize.”

Zaman ya jaddada muhimmancin amfani da ingantattun hanyoyin kula da Tela Maize, sa ido kan yawaitar ƙwari da kuma dabarun ɗorewar yaƙi da su domin tabbatar da ingancin fasahar masarar da ke da juriyar ƙwari.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a horarwar su ne zaman tambayoyi da amsoshi mai cike da mu’amala, inda mahalarta suka gabatar da tambayoyi masu alaƙa da aikace-aikace tare da bayyana abubuwan da suka fuskanta a gonaki.

Cibiyar IAR ta jaddada aniyarta na ci gaba da ƙarfafa samar da amfanin gona ta hanyar bincike, ƙirƙire-ƙirƙire, gina ƙwarewa da kuma yaɗa fasahohin noma masu ɗorewa.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Soyayyar Liverpool Ba Za Ta Taɓa Gushewa Daga Zuciyata Ba – Salah

Soyayyar Liverpool Ba Za Ta Taɓa Gushewa Daga Zuciyata Ba – Salah

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.