ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Na Neman Zunzurutun Kudi Kimanin Naira Tiriliyan 1 Don Gudanar Da Zaben 2027

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
7 months ago
inec

Hukumar zaBe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da majalisar kasa cewa tana bukatar naira biliyan 873.78 don gudanar da zaBen 2027. Haka nan kuma hukumar ta bukaci karin naira biliyan 171 don taimaka wa ayyukanta a shekarar 2026.

Naira biliyan 873.78 da aka tsara don gudanar da zaBukan shekarar 2027 yana nuni da karuwa mai yawa daga naira biliyan 313.4 da gwamnatin tarayya ta saki don gudanar da zaBen g 2023.

  • Tsarin Siyasar Kano: Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura…
  • Sashen Sayayya Da Kashe Kudade Na Kasar Sin Na Samun Bunkasa Ba Tare Da Tangarda Ba A Hutun Bikin Bazara

Kasar za ta gudanar da zaBe a shekarar 2027, yayin da jihohin Ekiti da Osun za su gudanar da zaBen gwamna a wannan shekarar, tare da zaBen shugabannin kananan hukumomi a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma zaBen cike gurbi.

ADVERTISEMENT

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana wannan yayin da yake gabatar da kasafin kudin hukumar na 2026 da kuma kiyasin kashe kudi don zaBukan 2027 a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokoki kan harkokin zaBe a Abuja.

A cewar Amupitan, kasafin kudin zaBe na naira biliyan 873.78 ya kunshi gudanar da dukkan zaBukan 2027, yayin da naira biliyan 171 ta 2026 za ta tallafa wa ayyukan yau da kullum, ciki har da zaBukan cike gurbi da zaBukan gwamnoni a wannan shekarar.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

A cewarsa, kasafin kudin zaBe da aka gabatar bai hada da sabon bukata daga hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) ba, wanda ta neman karin alawus ga masu yi wa kasa hidima da ke aiki a matsayin ma’aikata na wucin gadi a lokacin zaBe.

Ya bayyana cewa duk da cewa ba a gabatar da cikakkun bayanai na wasu batutuwan ba, kasafin kudin zaBen na kusan naira tiriliyan 1 an tsara shi a cikin manyan sassa biyar.

“Naira biliyan 379.75 an ware su ne don gudanar da ayyukan yau da kullum, naira biliyan 92.32 an ware su ne don ayyukan gudanarwa, naira biliyan 209.21 an ware su ne don kudaden da za a kashe a Bangaren fasaha, naira biliyan 154.91 don kudaden da za a kashe na babban zaBe da kuma naira biliyan 42.61 don kudade zarga-zirgan ma’aikata,” in ji Amupitan.

Ya bayyana cewa an shirya kasafin kudi a bisa tsarin sashe na 3(3) na dokar zaBe ta 2022, wanda ya umurci hukumar da ta shirya kasafin kudin zaBe akalla shekara guda kafin babban zaBe.

A 2026, Amupitan ya bayyana cewa ma’aikatar kudi ta bayar da kasafin kudi na naira biliyan 140, amma ya kara da cewa INEC na ba da shawarar jimillar kashe kudi na naira biliyan 171.

Jimillar kudaden ya hada da naira biliyan 109 kudin ma’aikata da naira biliyan 18.7 don ayyukan yau da kullum, da naira biliyan 42.63 don ayyukan da suka shafi zaBe da naira biliyan 1.4 don gudanar da manyan ayyuka.

Har ila yau, ya gano rashin samun cibiyar sadarwa ta musamman a matsayin babban kalubale na aikin hukumar. Yana kara da cewa idan hukuamar ta haBaka nata tsarin hanyar sadarwa, ‘yan Nijeriya za su kasance cikin yanayi mai kyau wajen sa idan akwai wata matsala ta fasahar sadarwa.

A yayin jawabi a zaman, Sanata Adams Oshiomhole ya ce ka da hukumomin waje su tsara tsarin kasafin kudi ga INEC, la’akari da muhimmancin aikin da take da shi. Ya yi kira a ajiye tsarin kasafin kudi mai rikitarwa.

Ya yi kira ga majalisar kasa ta hada kai da Shirin kudi na INEC don kauce wa yiwuwar karancin kudi a lokacin gudanar da zaBe.

Haka kuma, wani dan majalisar wakilai daga Jihar Edo, Billy Osawaru, ya nemi a sanya kasafin kudin INEC a kan babban jigo kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada, tare da sakin kudin gaba daya a kan lokaci domin ba da damar yin shiri zaBen 2027 a kan lokacin da ya dace.

Kwamitin hadin gwiwa ya amince da wani kudiri da ke ba da shawarar sakin kasafin kudin shekara-shekara na kwamitin sau daya.

Kwamitin ya kuma ce zai duba bukatar NYSC na kimanin naira biliyan 32 don kara kudin alawus din mambobin hukumar zuwa naira 125,000 kowanne lokacin da aka dauke su don ayyukan zaBe.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan INEC, Simon Lalong, ya tabbatar da cewa majalisa za ta yi aiki tare da hukumar don tabbatar da cewa ta samu goyon bayan da ya dace wajen gudanar da zaBen 2027 cikin nasara.

Haka kuma, shugaban kwamitin majalisar dokoki kan al’amuran zaBe, Bayo Balogun, ya yi alkawarin goyon bayan dokokin amma ya yi gargadi ga kwamitin ka da ya dauki alkawuran da zai iya kasa cikawa.

Ya tuna cewa a lokacin zaBen 2023, INEC ta bayar da tabbacin cewa za a dora sakamakon zaBe a shafi INEC, wanda hakan ya tabbacin da cewa ana iya sa ido kan sakamakon zaBe a kan lokaci.

“Na’urar saka sakamakon zaBe ba ya cikin dokar zaBe ko kadan, yana cikin dokokin INEC ne kawai. Don haka, a yi hattara yadda za a yi alkawaruka,” in ji Balogun.

Inec
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Inec
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamnan Radda Ya Rantsar Da Sabon Mai Shari’a, Khadi Mustapha Salisu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.