ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsarin Siyasar Kano: Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura…

by Sani Anwar and Sulaiman
7 months ago
Siyasar kano

A bayyana ne yake, abin da ya faru jiya a wurin taron bikin karBar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa cikin jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, wanda ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kàsa Kashim Shettima, GCON, wani ma’auni ne da yake haska wanda ya fi shiri a kan zaBen shekara ta 2027, tsakanin gwamna da jagororin APC a Jihar Kano.

Tashin farko, idan mutum ya yi nazarin taron zai fahimci cewa; da yawa daga cikin wadanda suka jagoranci shirya taron a Bangaren gwamna, ko dai sun nuna sakaci da lalaci, ko suna da raunin fahimtar yadda gwagwarmayar siyasa take, ko kuma a harkar tasu akwai zunzurutun rashin kwarewa.

  • Amurka Ta Kwace Kadarorin ‘Yan Nijeriya 8 Masu Alaka Da Boko Haram
  • Sultan Ya Jagoranci NSCIA Wajen Neman Sake Fasalin Jadawalin Zaben 2027 Cikin Gaggawa

Na yi zaton ganin dandazon masu jajayen huluna sun mamaye wurin. Kasancewar har yanzu, ita ce wani sitamfi na magoya bayan gwamnan, kafin daga nan zuwa wani lokaci a cire ta baki-daya. Samun yawaitar ko ruwan masu jajayen huluna a wajen, shi ne zai nuna karfin gwamnan da jama’arsa. Wanda hakan na nufin, gwamna yana tare da dandazon jama’ar da suka shiga APC tare, amma kuma sai aka samu saBanin haka.

ADVERTISEMENT

Abubuwan da suke yawo da falfali a wajen, riguna ne da huluna na masu dauke da sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar APC. Tun kuwa daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, har zuwa tituna, inda Mataimakin Shugaban Kàsa da manyan baki suka biyo a hanyarsu ta isa filin wasa na Sani Abacha, wajen taron.

Ina son tuna wa Gwamna Abba cewa; ya kamata a ce ya fi kowa tuna daga inda ya fito, sannan kuma mene ne hatsarin wajen. Wani abin da na kara lura da shi shi ne, da a ce alhakin wannan taron kawai an bar shi a hannun gwamna ne, shi kuma ya wakilta wadanda ta Bangarensa ya ba nauyin yin tasu hoBBasar a wajen wannan taro, da kuwa tabbas ba a samu nasarar da aka iya samu ba yanzu.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Amma fa shi gwamna a kan kansa, ya yi iya nasa. Abin tambayar shi ne, ina mutanensa da ya dora musu nauyin harkar wadanda ke cikin gwamnatin tasa?

Wannan taron babu shakka ya kara haska tare da tabbatarwa kowa irin tsari da tasiri da tsari na jiga-jigan APC da gwamna ya tarar a jam’iyyar suke. Ko ina ka kalla, abin da kawai za ka gani su ne magoya baya nata taken alkiblar siyasarsu. Kuma kashi 80 cikin 100 na magoya bayan da suka fito, daga Bangaren manyan jam’iyyar APC suke.

Har ta kai ta kawo fa da yawa mutane sun fara tambayar cewa, ina shugabannin kananan hukumomi? Ina kwamishinoni da mashawartan gwamna? Ina ‘yan majalisar da gwamna ya tawo da su, daga na jiha zuwa na tarayya? Ina makusantan gwamnan? Ina masu yi wa gwamnan fatan alhairi? Ina shugabannin Bangarorin hukumomin gwamnati? An yi wadannan tambayoyin ne saboda ba a ga BurBushinsu yadda ya kamata ba.

Wannan sakacin, na nuna rashin kyakkyawan shirin wayar da kai daga Bangaren shugabannin kananan hukumomi, musamman, wadanda bisa tsari da ake da shi ya kamata su taka gagarumar rawa wajen hada jama’a daga kananan hukumominsu. Wato daga tushe.

Allah Ya ji kan Murtala Sule Garo, ba don ya mutu ba. Sai nake tuna lokacin yana Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON), ko lokacin da yana matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, ko lokacin da yake matsayin Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyya mai mulki a lokacin. Tafiyar tasa akwai kyakkyawan haske, tsafta, tsari, jajircewa da kuma cika alkawura.

Ni a wajena, taron nan da aka yi ya bayyana karfi, tasiri da darajar mutane hudu ko biyar da na ga jajircewarsu a lokacin taron. Abin da nake nufi shi ne, su wadannan mutanen na APC, wadanda Gwamna Abba ya tarar a jam’iyyar a wannan lokacin da aka samu juyawar yanayin siyasar a Jihar Kano.

Su ne, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ta Kasa, Sanata Barau I Jibrin, CON, Mataimakin Dan Takarar Gwannan Kano na Jam’iyyar APC, a zaBen shekara ta 2023, Murtala Sule Garo, Shugaban Kwamitin Raba Arzikin Kasa na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, Babban Daraktan Cibiyar Nagartar Ayyuka Ta Kasa, Baffa Babba Dan Agundi da wakilin al’ummar Kananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Alhassan Ado Doguwa.

Wadannan mutane da na ambata, da hoBBasar da suka yi a lokacin taron, sun tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa; jam’iyyar APC har yanzu a raye take, kuma tana motsawa sosai a Jihar Kano.

Sannan wannan wani sako ne da aka aika wa Shugaban Kàsa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, cewa; tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, CFR, har yau har gobe tsayayye ne, kuma bai yi kasa a gwiwa ba.

Gudunmawar da mutanen nan biyar masu kima da na ambata a sama suka bayar, ya kamata ya zama wata izina ga gwamna, domin ya san su wa ya kamata ya kara rikewa a jihar. Dukkaninsu sun ba da gagarumar gudunmawa, sun kuma nuna dabarun siyasa, kwarewa da yin aiki da gwamna bisa jajircewa, kan abin da za a yi a lokacin da ya kamata.

Don haka, samun nasara da matakan samun nasarar, sau da yawa a hannun gwamna suke. Idan na yi maganar nasara, ina hangen shekara ta 2027.

Idan na tawo kasa, bayan bayyana sunayen Barau, Garo, Abba Bichi, Doguwa da Dan Agundi, sai na kalli tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birni da Kewaye, Fa’izu Alfindiki da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai na yanzu, Abdullahi Waiya, wadanda su ma sun yi abin da ya dace, sun yi aiki kwarai da gaske a Bangarensu.

Na yi matukar jinjina wa kokarinsu, jajircewa da cikakkiyar biyayya da suka nuna, tun kafin ma taron da lokacin taron da bayan taron. Kazalika, na jinjina wa kyakkyawan aikinsu a matsayin ‘yan wasan da ake bukata.

Idan na kara tawowa kasa dai, dole a yaba wa jajircewa, biyayya da goyon bayan Kwamared Magaji Kabiru Gulu daga Rimin Gado da kuma wannan matashin Aminu Dahiru, shi kuma daga Karamar Hukumar Gwale. Idan kuma ana maganar hada gangami na mutane, ina da yakinin za su bayar da gagarumar gudunmawa daban-daban.

Ina bayar da shawara ga mai girma Gwamnan Jihar Kano, Yusuf, da ya yi duban tsanaki a cikin shugabannin kananan hukumominsa 44. Ta bayyana kwarai cewa, akwai gazawa matuka ta fuskar hada-hadar shirya gagarumin taro irin wanda ya wakanan.

A jama’arka a wajen wannan taro, mai girma gwamna gaskiya akwai nakasu, rashin kwarewa, sakaci, rikon sakainar kashi, kan rashin shigar da jama’a cikin al’amura. Yayin da gwamna ya kamata ya fuskanci kalubalen da ke gabansa da gasken gaske, yin aiki da jama’ar APC, ya zama abin da bai kamata a kaucewa ba.

Siyasar kano
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
Siyasar kano
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Sashen Sayayya Da Kashe Kudade Na Kasar Sin Na Samun Bunkasa Ba Tare Da Tangarda Ba A Hutun Bikin Bazara

Sashen Sayayya Da Kashe Kudade Na Kasar Sin Na Samun Bunkasa Ba Tare Da Tangarda Ba A Hutun Bikin Bazara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.