ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kidayar Jama’a Da Harkar Ilimi

by Leadership Hausa
6 months ago

Ta yaya ne gwamnati za ta fahimci adadin makarantu, ajujuwa da sauran kayan aikin karatu da garin ake da bukata sama da garin B?. Hatta adadin dalibai wadanda kanana da manyan makarantunmu ya kamata su dauka a duk Shekara, na da alaka ta kud da kud, da sanin hakikanin adadin yawan jama’ar kasa.

Ba ya ga sanin adadin yawan dalibai da ya kamata makarantun su dauka, wajibi ne ma gwamnati ta kwana da sanin adadin wadanda ba sa zuwa makarantar. Yayin da gwamnati ke da cikakken adadin yawan wadanda ba sa zuwa karatu, a duk sa’adda za ta bijiro da wata manufa, ta mayar da yara makaranta, idan ba ta da hakikanin adadin yawansu, tabbas wannan shiri na gwamnati zai zamto makahon shiri ne!

  • Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami
  • Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Kasar Sin Sun Samun Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba a Watanni 11 Na Farkon Bana

Rashin sanin hakikanin adadin jama’ar Nijeriya a yau, ya taimaka ainun, wajen rashin samun nasarar aikace-aikace da sauran wasu manufofi da gwamnatoci a matakai iri daban-daban suka sanya a gaba. An wayi gari, kowace makaranta na yin kintacen abinda za ta iya dauka ne, a duk karshen Shekarar daukar sabbin dalibai. Hatta ita kanta gwamnati, da tana da cikakken adadin yawan jama’ar Kasa a hannu cifcif, tana iya sanya-baki ga makarantunmu, wajen hakkake adadin wadanda ya kamata a dauka sabon zangon karatu. Yanzu haka a yau, gwamnatin taraiyar Nijeriya, jihohi hada da kananan hukumomi, ba su da wani cikakken bayanai da za su iya hakkake musu adadin yawan al’umar Kasa. Duk wasu abubuwa da za su gudanar, wadanda ke da jibi da muhimmancin sanin adadin yawan jama’a, sai dai su yi kintace ne kurum. Ko dai su gina lissafinsu ne bisa lissafin wasu hukumomi na Duniya, irin su “United Nations”, “WHO”, “UNICEF” da sauransu. Koko ma su gina lissafin nasu a kan tubalin sakamakon kidayar jama’a ta karshe da aka yi a wannan kasa, Shekaru goma sha-takwas (18) da suka gabata, 200b.

ADVERTISEMENT

Sanin adadin malaman makaranta da za a kai makarantu, koko wata makaranta, dole yana da alaka da sanin hakikanin adadin dalibai da wannan makaranta za ta dauka, ko take da su, a matsayin dalibai. Bugu da kari, su kansu adadin ajujuwa da gwamnati za ta samar, suma suna da alaka ta kusa, da wajibcin sanin adadin dalibai da za a dauka. Sannan, idan makarantun na kwana ne, suma, suna da muradin sanin iya adadin daliban da makarantar za ta dauka a matsayin dalibai, don sanin adadin dakunan kwanan dalibai da za a samar. Mai karatu ya sani cewa, duka wadannan lissafe-lissafen adadi da ake ta faman gabatarwa, ba za a yi su cikin nasara kuma a ilmance ba, dole ne sai an fahimci hakikanin adadin yawan jama’ar kasa, wanda sanin adadin yawan jama’ar kasa kuwa, ya dogara ne kacokan a kan gudanar da aikin kidayar jama’a ta kasa baki daya akai akai (duk bayan Shekaru 10).

Duk wani shiri, ko wata manufa “policy” da gwamnatin karamar hukuma, ko jiha, koko ta tarayya za ta kirkira game da inganta fannin na ilimi, zai zamto gungun shiri ne, muddin gwamnati ta saba lambar sanin hakikanin adadin yawan jama’arta!. Ke nan, ita kanta wata sabuwar manufa, ko wani sabon shiri na gwamnati game da bunkasar ilimi, na da matukar bukatar son sanin hakikanin adadin yawan jama’ar kasa ko waje, don kaucewa, kamfa, ko daban-kwalo, tare da samun cikakkiyar nasarar da aka nufata.

LABARAI MASU NASABA

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

Duk kasar ta gaza sanin adadin yawan mutanenta, labudda a yi ta faganniya cikin duk wani abu muhimmi da gwamnatin kasar ta sanya a gaba, ba ya ga sabgar ilimi. Akwai misalai bila-haddin, sai dai wajibi ne a takaita.

 

Kidayar Jama’a Da Harkar Tsaron Kasa

Tamkar irin yadda hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta bukaci duk likita guda, ya jibinci duba marasa lafiya dari shida (1:b00) a karkashisa, haka ma a bangaren na tsaro, majalisar dinkin Duniya ta nemi duk wani jami’in tsaro (dan sanda) guda, zai rika bibiyar lamuran akalla mutane dari hudu da hamsin (police-to-citizen ratio, 1:450) ne. Ta yaya ne za a iya faiyacewa tare da dabbaka wannan ka’ida, ba tare da sanin hakikanin adadin yawan jama’ar Kasa ba?. Faro tun daga daukar sabbin jami’an tsaron, sai an san yawan adadin yawan jama’ar Kasa, daga nan ne ma za a dora sanin hakikanin adadin yawan jami’an tsaron da za su wadaci Kasa aiki. Maimakon jami’i guda jama’a 450, yanzu haka a Nijeriya, duk jami’in tsaro guda, an dora masa alhakin kulawa da mutum dari shida (1:b00) ne.

Saboda rashin aza abu bisa turbarsa ne a yau a Nijeriya, Shekara da Shekaru an rasa iya dibar hakikanin adadin jami’an tsaron da ake da bukata, don kawo zaman lafiya a Kasa. Babban sifeton “yan sandan wannan Kasa, Kayode Egbetokun, da kansa ya labarta cewa, wannan Kasa tamu a yau, na bukatar karin adadin jami’an tsaro har kimanin dubu dari da casa’in (190,000). Tun da harkar daukar sabbin jami’an tsaron ta zamto canki-in-canka ne, kowane shugaba ya zo, sai dai ya kwashi adadin mutanen da ya ga dama ne, ko da yake da muradi. Ko sun wadatar, ko ba su wadatar ba oho!. Irin wannan dalili na rashin dibar jami’an tsaron wadatattu, ba karamin miki ne zai yi wa sabgar tsaron kasa ba.

Da kasar tana da hakikanin adadin yawan jama’arta, babu wata wahalarwa, ko wani aikin baban-giwa da za a yi, a duk lokacin da bukatar daukar jami’an tsaron ta zo, nan take ne za a fahimci adadin yawan da sune za su cika waccan ka’ida da majalisar dinkin Duniya ta aje, wajen tabbatar da adadin yawan jami’an tsaro, bisa la’akari da adadin yawan jama’ar kasa. A fili ne yake cewa, da yawa daga Kasashen da suke dabbaka irin wadancan ka’idoji na hukumomin Duniya, ta hanyar mayar da hankali bisa gudanar da aikin kidayar jama’a a wurarensu, sun kere Nijeriya ci gaba ta fuskoki da dama. Harkar lafiyarsu, iliminsu, tattalin arzikinsu da tsaronsu, duka sun yi wa Nijeriya shal!.

Ba wai daukar adadin yawan jami’an tsaron ne kawai kan taimaka wajen dakile ta’adar ta’addanci ba, hatta sanin adadin yawan jama’ar wuri, banbance-banbancensu, sanin hanyoyin samunsu, Shekarunsu da sauransu, kan taimaka wajen sanin duk wasu bakin-hauren da za su shigo cikin Kasa da wata boyaiyar manufa maras kyawo. Rashin sanin hakikanin jama’ar Karkara, tare da sama musu ababen more rayuwa, na daga dalilan da ke sanya su fantsama cikin birane, wanda a karshe ake kaiwa ga cunkushewa wuri guda. Duka wadannan ababen ki a kan magance afkuwarsu ne ta fuskar gudanar da sahihiyar kidayar jama’a a kasa.

Hatta a bangaren samun ci gaban tattalin arzikin Kasa, sanin hakikanin adadin yawan jama’ar kasa, kan taimaka wajen samun ababen more rayuwa masu tarin yawa daga gwamnati. Ta yaya ne jiha kamar Kano da ta kusan ninka jihar Nassarawa har kimanin sau hudu, za a gabatar musu da ababen more rayuwa adadi iri guda?. Idan jihar Nassarawa na da bukatar a sama mata da megawat na wutar lantarki dari biyar ne. Ke nan, jihar Kano na da bukatar a kai mata megawat na wuta dubu biyu ne. Mai yi wa, irin wannan dalili ne ma ya sa a lokacin jamhuriyar siyasa ta biyu (2nd Republic, 19b0 – 19bb) ake raba arzikin Kasa ga jama’ar kasa, bisa la’akari da yawan mutane da kowace jiha a kasar take da. Bugu da kari, shi sanin adadin yawan mutane da wata jiha ke da shi, ba ita kadai ce za ta amfanu da hakan ba, hatta gwamnatoci ma za su amfana, ta hanyar sake fasalta tsarin samun kudadenta na shiga a irin wadannan wurare dake dauke da jama’a jingim. Haka ma masu cutar yatsun hannu, ko na rashin gani da sauransu, adadinsu kan banbanta daga waje ne zuwa waje, saboda haka, bayar da tallafi iri guda ga daukacin jihohi 3b na Kasar, hada da Abuja, zai zamto tamkar wani rashin adalci ne. Ke nan, gudanar da kidayar, zai zamto hatta masu bukata ta musamman ma za su shana ne, ma’ana, za su kurbi romon dauki daga gwamnatocin gida da na waje, sama da irin yadda suke samu a yau.

Mabanbantan aji-aji na mutane, misali masu bukata ta musamman, kan mori agaji daga Kasa da kuma sauran kasashen ketare, yayin da aka san hakikanin adadinsu a wuri. Za a san adadin nasu ne ta hanyar gudanar da kidayar jama’a a Kasa.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu
  • Leadership Hausa
    Ikirarin Cewa Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sokoto, Nauyi Ne Ga Jihar Zamfara Da Jam’iyyar APC Ba Ta Da Tushe

MASU ALAKA

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
Bakon Marubuci

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
Bakon Marubuci

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

May 27, 2026
obi
Bakon Marubuci

Su Wa Ke Fatattakar Obi Da Kwankwaso?

May 16, 2026
Next Post
2027: Sauya Sheka Zuwa APC Ba Zai Taimaki Tinuba Yin Tazarce Ba – Jam’iyyar ADC

SDP Ta Gargadi INEC Kan Yin Katsalandan A Harkokin Jam’iyyar

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN Ya Shaida Gamsuwar Masu Bayyana Ra’ayoyi Da Gudunmawar Sin Game Da Tsarin Jagorancin Hakkin Bil’adama

Binciken CGTN Ya Shaida Gamsuwar Masu Bayyana Ra’ayoyi Da Gudunmawar Sin Game Da Tsarin Jagorancin Hakkin Bil’adama

June 11, 2026
Kasar Sin Ta Sanar Da Sanya Takunkumi A Kan Ministan Tsaron Kasar Philippines Da Iyalansa

Kasar Sin Ta Sanar Da Sanya Takunkumi A Kan Ministan Tsaron Kasar Philippines Da Iyalansa

June 11, 2026
An Rufe Makarantu A Mexico Saboda Fara Gasar Kofin Duniya

An Rufe Makarantu A Mexico Saboda Fara Gasar Kofin Duniya

June 11, 2026
An Kaddamar Da Dandalin Kasa Da Kasa Game Da Tsarin Jagorancin Hakkin Dan Adam Na Shekarar 2026 A Beijing

An Kaddamar Da Dandalin Kasa Da Kasa Game Da Tsarin Jagorancin Hakkin Dan Adam Na Shekarar 2026 A Beijing

June 11, 2026
Kwararrun Sin Da Na DRC Sun Tattauna Matakan Hadin Gwiwa Na Dakile Cutar Ebola

Kwararrun Sin Da Na DRC Sun Tattauna Matakan Hadin Gwiwa Na Dakile Cutar Ebola

June 11, 2026
Majalisa Ta Goyi Bayan CBN Kan Sauya Fasalin Naira Bayan Tafka Muhawara 

Majalisar Dattawa Ta Tswaita Aiwatar Da Kasafin Kuɗin 2025 Zuwa 30 Ga Watan Satumba

June 11, 2026
Majalisa Ta Amince Da Ƙudirin Dokar Kafa ‘Yansandan Jihohi.

Majalisa Ta Amince Da Ƙudirin Dokar Kafa ‘Yansandan Jihohi.

June 11, 2026
Shugaban Sin Na Jagorantar Bunkasa Dangantakar Sin Da Koriya Ta Arewa A Sabon Zamani

Shugaban Sin Na Jagorantar Bunkasa Dangantakar Sin Da Koriya Ta Arewa A Sabon Zamani

June 11, 2026
Nijeriya da Habasha Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dawo Da Fursunonin Nijeriya Sama da 100

Nijeriya da Habasha Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dawo Da Fursunonin Nijeriya Sama da 100

June 11, 2026
Za A Kammala Aikin Bututun Iskar Gas Na AKK A Disambar 2024 – NNPC

Na Yi Matuƙar Mamakin Sammaci A Kaina – Mele Kyari

June 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.