ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kiwon Shanu A Titunan Abuja Barazana Ne Ga Tsaron Nijeriya —Wike

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya nuna damuwarsa kan yadda shanu ke yawo a titunan Abuja, yana mai bayyana lamarin a matsayin batun tsaron kasa.

Ministan ya jaddada cewa bai kamata a bar dabbobi suna yawo ba tare da kulawa a babban birnin kasar ba.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin tattaunawarsa ta wata-wata da manema labarai a Abuja, lokacin da yake amsa tambayoyi kan karuwa da aka samu na shanu a wasu sassan birnin duk da kokarin da ake yi na inganta gine-gine da kyawun birnin.

ADVERTISEMENT

Da aka tambaye shi game da shanun da ke kiwo a filayen ciyawa da kuma yawo a kan tituna a Abuja, Wike ya ce: “Wannan batu ne da ya shafi tsaron kasa.”

Lokacin da aka kara matsa masa ya bayyana yadda lamarin ke da alaka da tsaron kasa, sai ya amsa da cewa: “A’a, a’a, a’a. Dole ne mu fuskanci gaskiya.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

A cewarsa, manufar Gwamnatin Tarayya ta kiwon dabbobi a ruga (ranching) ita ce hanya mafi dacewa wajen magance matsalar.

“Daya daga cikin abubuwan da muka fara yi lokacin da muka zo shi ne bin umarnin Shugaban Kasa cewa mu aiwatar da tsarin kiwon dabbobi a ruga domin mu fitar da shanu da sauran dabbobi daga cikin birni,” in ji shi.

Yana bayyana halin da ake ciki a matsayin abin takaici, Wike ya kara da cewa:

“Abin na bata wa ido rai. Bai dace ba. Ba abu ne mai kyau ba.”

Ministan ya ce a kasashen da suka ci gaba ba a barin dabbobi suna yawo cikin birane.

“Muna da kasashe masu ci gaba da ke kiwon shanu. Sai dai idan ka je wuraren da ake kiwon su za ka gan su. Ka je Saudiyya. Ka je sauran manyan birane. Ba za ka ga shanu suna yawo a can ba,” in ji shi.

Wike ya kuma koka cewa duk lokacin da gwamnati ta fito da wasu manufofi domin magance irin wannan matsala, mutane kan yi musu mummunar fahimta ko kuma su mayar da lamarin siyasa.

“Da zarar ka fara aiwatar da wasu manufofi, mutane sai su ce wai ana yin hakan ne saboda wani dalili. A’a, a’a, a’a. Batu ne na tsaron kasa,” in ji shi.

Ministan ya kuma yi magana kan matsalar kasuwanci a kan tituna, bara da sauran abubuwan da ke kawo cikas a tsakiyar birnin.

A cewarsa, Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) na ci gaba da kokarin korar ‘yan kasuwar da ke kasuwanci a bakin tituna da wuraren da ba a amince da su ba, amma tana bukatar karin goyon bayan jama’a domin ci gaba da nasarar wannan aiki.

“Idan ka ga an ware maka wuri don yin kasuwanci, to a can ya kamata ka yi. Ba wai ka zauna a ko’ina ba. Daga baya sai ka ga an mayar da wurin kasuwa alhali ba kasuwa ba ce. Wannan ma wani nau’in kawo cikas ne,” in ji shi.

Wike ya kara da cewa matakan da gwamnati ke dauka na da nufin kare martaba da kyawun babban birnin kasar.

“Mun dade muna wannan aiki kuma za mu ci gaba da yi. Amma muna bukatar goyon bayan kafofin yada labarai domin wayar da kan jama’a cewa abin da muke yi yana cikin muradun al’umma baki daya.

“Wannan shi ne babban birni guda daya da Nijeriya ke da shi. Ba za mu bari a lalata shi ba kawai saboda wani yana neman hanyar samun abin da zai ci yau da kullum. Neman abin rayuwa ba yana nufin a karya dokokin da aka kafa ba,” in ji ministan.

Wike
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
Labarai

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Next Post
Labarin Yin Yuzhen: Sin Tana Hadin Gwiwa Da Ketare Don Cika Alkawarin Kiyaye Muhallin Duniya

Labarin Yin Yuzhen: Sin Tana Hadin Gwiwa Da Ketare Don Cika Alkawarin Kiyaye Muhallin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.