ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kun San Wadannan Abubuwan Game Da Mazajenku?

by Leadership Hausa
6 months ago

Daga Bilkisu Tijjani Kasim

Yau tsaraba ce ga mata kan abubuwan da ya dace su sani game da mazajensu na aure.

Da farko kafin mu yi nisa, ya kamata mace ta yarda mijinta shi ne shugaba a kanta (wannan wajibi ne ba zabi ba), ko da kuwa ta girme shi da shekaru, ko ta fi shi kudi, ko ilimi, ko matsayi, ko karfi ko dai wani abu na rayuwa. Ki tuna fa shi ne ya je har gidanku ya nuna sha’awar kasancewa tare da ke na tsawon wani lokaci da ba shi da karshe sai fa in mutuwa ta zo.

Shi ne yake da hakkin kula da ke dangane da ci, sha, tufafi, matsuguni da kuma biya miki sauran bukatun rayuwa da babu wanda ya isa ya biya miki ban da shi.

ADVERTISEMENT

Akwai abubuwa da dama wadanda mata ya kamata su sani game da mazajensu, ga kadan daga cikin su kamar haka:

Yin kasa da sauti in kina magana da shi: Mace ta gari ita ce wacce ba ta daga muryarta idan tana magana da mijinta, ko da kuwa ranta ya baci. Yin hakan zai iya fusata shi kuma ta yiwu ma har ya yi abin da bai kamata ba. Idon kika fahimci cewa ya hau sama wato ransa ya baci, sai ke kuma ki sauko kasa.

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

Ki ba shi hakuri in kin yi masa laifi: Dole ne mace in ta yi laifi ta bada hakuri. Wasu matan in sun yi laifin ma aka fada musu sai su fara musu, suna kokarin kare kansu. Mace ta gari ita ce wacce in ta yi laifi za ta yarda ta yi kuma ta bada hakuri.

Daukar shawararsa: Idan mijin ki ya baki shawara a kan wani abu ya kamata ki girmama ra’ayinsa in har bai ci karo da addini ba. Wannan shi zai tabbatar masa da cewa kina girmama shi.

Wannan yana da matukar muhimmanci. Wasu matan kafarsu kamar tana kaikayi, miji yana fita za su dauki gyale sai gidan makota ko gidan kawaye. Gaskiya hakan ba hali ne na gari ba.

Ki sani dole ne in za kika fita, ki fita da izinin mijinki, kuma wajibi ne ki tsaya a iya inda kika ce za ki je. Wasu matan za su tambayi izinin zuwa gida daya ko biyu, amma za su iya shiga gidaje goma.

Idon kina fita aiki, ya kamata ki kiyaye kanki daga abokan aikinki, ki rike amanar mijinki a wurin da baya nan. Wasu mazajen sun amince wa matansu amma su matan za su iya cin amanarsu.

Ki sani fa wasu mazan za su rinka kula ki ko da kuwa sun san kin yi aure kuma sun san mijin naki, musamman ma in kina da kyau kuma ke fara ce, kin san mafi yawan maza suna son farar mace har ma za ki ji wasu suna cewa “fara ko ‘yar gidan sarkin mayu ce”. Dole ki lura da irin wadannan domin komai kamun kanki sun san yadda za su shawo kanki domin ki kula su.

Su ma matan da suke fita aiki, ku ji tsoron Allah in kun fita daga gida kar ku tsaya ko ina sai wajen aikinku, haka kuma in kun dawo kar ku tsaya a ko ina sai gidanku. Wasu matan suna amfani da aikinsu sai su shiga kasuwanni su yi ta yawo da sunan sayayya suka je, gaskiya hakan ba shi da kyau.

Ki tuna fa ‘ya’yanki in sun dawo daga makaranta suna bukatar ganinki, haka kuma mijinki ma in da wuri yake dawowa daga wajen aikinsa yana bukatar ganin ki tare da kulawa daga wajenki.

Ya kamata mata su tuna cewa aure Ibadar Allah ce, yana da kyau su kyautata wajen zamantakewa da miji.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.