ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kofin Duniya: Tikitin Kallon Wasan Karshe Ya Kai Sama Da Naira Miliyan 16

by Abba Ibrahim Wada
5 months ago
Kofin

A lokacin da aka bude shafin sayar da tikitin zuwa kallon gasar cin kofin duniya, mutane da dama sun ga ana sayar da tikitin kallon wasan karshe kan Dala 10,990. Ana kyautata zaton cewa shi ne tikitin kallon kwallon kafa mafi tsada kuma a lokacin da aka bai wa Amurka da Canada da kuma Medico damar karbar bakuncin gasar, sun ce tikitin kallon wasan karshe ba zai haura Dala 1,550 ba.

Lokacin da aka fara sayar da tikiti ga magoya bayan tawagogin wadannan kasashe a watan Dismaba, tikitin da ya fi tsada shi ne wanda kudinsa ya kai Dala dubu 8,680. Farashi ya sake yin sama a ranar Laraba lokacin da aka fara sayar da tikitin kallon wasan karshe.

An sayar da tikitin wasan karshe na gasar Kofin Duniya a Katar a 2022 kan Dala 1,604. Abu ne mai wuya a gano abin da ya janyo tikitin ya yi tsadar gaske saboda FIFA ba ta taba fitar da yadda take tsara farashin tikiti ba. A karshen shekarar da ta gabata an kwatanta farashin tikiti da aka fitar a matsayin “cin amana mai girma”.

ADVERTISEMENT

A watan Disamba, FIFA ta sanar da wasu tikiti da ake sayar wa kan Dala 60.

Sannan yana da matukar wahala a iya gane yadda tsarin saka farashin tikitin yake saboda babu bayanai da suka kamata. Yin duba kan shafin sayar da tikiti na FIFA da kuma ganin abubuwan da suka rage da kuma abin da ake caza yana nuna abu mai kyau. Sai dai, hakan ba yana nufin cewa akwai tikiti masu tsada ba, ko kuma idan akwai masu rahusa wadanda za a iya saya.

LABARAI MASU NASABA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Daga abin da aka lura, tikitin wasan karshe na gasar Kofin Duniya ya karu da kashi 38 lokacin da aka fara sayar da shi, ba kamar lokacin da aka fitar da shi a watan Disamba ba. Baya ga tikitin mataki na farko da ake sayarwa kan Dala 10,990. Tikitin mataki na biyu kuma ya karu da kashi 32.78 daga Dala 5,575 zuwa Dala 7,380. Tikitin mataki na uku kuma ya karu da kashi 38.23 daga Dala 4,185 zuwa Dala 5,785.

Har ila yau, Fifa ba ta ba da sanarwa kan wasanni ba, ko kuma a farashi nawa za a sayar da su “lokacin da aka bude” sayar da tikiti. Wadanda suka ziyarci shafin sun lura da cewa an fi neman sayan tikitin manyan wasanni – ciki har da na manyan tawagogi da kuma na wasannin zagaye na falan daya da na kusa da na karshe.

Fifa ta sake bude shafin sayar da tikiti ranar Alhamis, kuma kamar yadda aka yi tsammani an samu karin farashi a tikitin wasannin da za a yi a Amurka da Canada. Dokokin Medico sun hana sake sayar da tikiti fiye da kima kuma duk wanda ya sayi tikiti zai iya sayar da shi kan farashi da yake so. Farashin tikitin da ya fi tsada shi ne na wasan karshe wanda ya kai Dala 82,780, inda mai karamin kudi ya kasance kan Dala 27,000.

Farashin tikitin wasan Ingila na farko da Croatia, wanda yake kan Dala 60, ya kai Dala 1,499 a shafin. Fifa na cazar dukkan masu saya da sayarwa da kashi 15.

Yadda FIFA ta gudanar da tsarin sayar da tikitin ya haifar da rudani da cece-kuce. Rashin tsari kan farashi da karancin bayanai, sun janyo wahala ga magoya baya wajen shirya wa gasar ta kofin duniya.

Kofin
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
Wasanni

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Next Post
Yadda Aka Gano Asibitocin Da Ke Yada Wa Yara Cutar HIV – Binciken BBC

Yadda Aka Gano Asibitocin Da Ke Yada Wa Yara Cutar HIV - Binciken BBC

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.