Rahotanni daga ƙasar Kamaru na cewa, mutane sama da 100 sun mutu sakamakon ruftawar wani wurin haƙar ma’adinan zinare a wani ƙauye da ke kan iyakar ƙasar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Talata a ƙauyen Zamboye da ke kusa da garin Garoua-Mboulaï na yankin Adamawa, inda kafofin yaɗa labarai na Kamaru da Afirka ta Tsakiya suka ce ana fargabar mutuwar mutane sama da 100, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Da sanyin safiyar wannan Laraba, magajin garin yankin Amadou Abdon ya tabbatar da zakulo gawarwakin mutane 107 daga cikin laka, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto.
A watan Maris ɗin da ya gabata, wani ɗan jarida da ya gudanar da bincike kan cibiyoyin haƙar gwal a yankin ya bayyana rohotanni masu tayar da hankali.
Wurin haƙar ma’adai a bakin Kogin Kadéï ya ƙunshi mutane da dama daga Afirka ta Tsakiya da Chadi da Mali da Burkina Faso da suka yi tururuwa domin aikin haƙar zinare ba bisa ka’ida ba.














