ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kujerar Shugaban Ƙasa Nake Buƙata A 2027 Ba Mataimaki Ba – Amaechi

by Leadership Hausa
9 months ago

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ƙaryata iƙirarin da ke alakanta shi da yiwuwar tikitin mataimakin shugaban ƙasa yak nema tare da tsohon mataimakin shugaba ƙasa, Atiku Abubakar a zaɓen 2027.

Ya ce shi kujerar shugaban ƙasar Nijeriya yake da buri kuma ba zai yi wa kowa mataimakin takara ba a zaɓen 2027.

  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
  • Dakta Soky  Amachree: Dan Kishin Kasa Jakada Nagari

Kalamun Amaechi ya biyo bayan maganganun da abokin Atiku, Dele Momodu, wanda ya nuna cewa Atiku na iya la’akari da tsohon gwamnan Jihar Ribas a matsayin mataimakin takararsa idan Peter Obi ya ƙi haɗewa da shi.

ADVERTISEMENT

A cikin wata hira da ya yi da ƴan jarida, Momodu ya yaba tasirin siyasar Amaechi, yana bayyana shi a matsayin babban mutum da ya taimaka wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari har ya samu nasara a 2015.

Da yake bayar da martani ta bakin mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Xavid Iyofor, Amaechi ya yi watsi da duk wata tattaunawa kan haɗin gwiwa da nufin sanya shi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa. Iyofor ya bayyana cewa Amaechi na ganin lokaci ya yi da yankinn kuduncin Nijeriya zai sake samar da shugaban ƙasa na gaba, don haka ya fara neman tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Ya ce, “Amaechi ba ya neman zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa ga kowa. Bai yi niyyar zama mataimakin shugaban ƙasa ga kowa ba kuma ba zai yi ba.

”Amaechi bai sanin da wannan ba, kuma ba zai shiga kowane tattaunawa ba don ya zama mataimakin wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba. Ko shakka babu Amaechi na neman zama shugaban Nijeriya ne ba wai don ya zama mataimakin wani ba.

“Ina shawartar ‘yan siyasa su bar kiran sunan Amaechi a wajen kowace tattaunawa kan wanda zai zama abokin takarar shugaban ƙasa,” in ji Iyofor.

Wannan ba shi ne karo na farko da Amaechi ya bayyana a niyyarsa a fili ba ta neman tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC ba. A watan Agusta, ya yi alƙawarin cewa ba zai iya januewa kowane ɗan takara ba yayin zaɓen fid da gwani na jam’iyyar, yana mai jaddada cewa mutane ne ya kamata su yanke shawara kan wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

A farkon watan Yuli, ya kuma bayyana cewa shirye yake na yin wa’adi guda na shugaban ƙasa don inganta tsarin karɓa-karɓa da samun kwanciyar hankali na siyasa idan aka zaɓe shi a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

“Da ba don saboda yarjejeniyara ba, amsar ko zan tsaya takara a matsayin shugaban ƙasa zai kasance eh ne kai tsaye.

“Amma mene ne muka amince da shi? Kowa ya ajiye burinsa. Barinmu shi ne fara samun jam’iyya. Barinmu mu gina jam’iyyar kafin a fara batu kan shugabancin ƙasa,” in ji shi.

Amaechi ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a shekarar 2022, inda ya zo na biyu bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ya lashe tikitin jam’iyyar a wancan lokaci.

Shugaban
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa

Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.