Wasu mazauna Jihar Kebbi sun tare babbar hanyar Jega zuwa Kontagora ranar...
Read moreDetailsShugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙalubalanci masu neman shugabancin Nijeriya da su...
Read moreDetailsKwamishinan Ƴansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya fayyace dalilin da...
Read moreDetailsƘungiyar tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai suna PBAT Door-to-Door, reshen Jihar...
Read moreDetailsAƙalla ƴan kasuwa 22 ne suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma...
Read moreDetailsTsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman...
Read moreDetailsWasu mambobin ƙungiyar “Tinubu Must Go” a Jihar Kano sun zargi rundunar...
Read moreDetailsJam’iyyar ADC a Jihar Jigawa ta nuna rashin amincewa da cire sunan...
Read moreDetailsReshen jam’iyyar NDC na Jihar Kano ya danganta rashin bayyanar sunan ɗan...
Read moreDetailsRa’ayin mutane ya banbanta musamman a kan takaddamar da ake yi ko kuma ta bullo tsakanin danwasa Cristiano Ronaldo da kociyan tawagar ‘yanwasan Portugal, Jorge Jesus. Sai dai magoya bayan Portugal sun fara ganin yadda tawagar ta buga wasa ba tare da Cristiano Ronaldo ba, bayan da kasar ta doke Denmark da ci 4-2 a gasar Nations League ranar Alhamis. Joao Cancelo da Goncalo Ramos ne suka bai wa bakin damar cin kwallo biyu, yayin da Mikkel Damsgaard da Rasmus Hojlund suka farke wa Denmark. Tsohon dan wasan Manchester United, Hojlund, ya yi murnar cin kwallon da ya ci da kwaikwayon salon yadda Ronaldo ke yi 'Siuuu' da zarar Ronaldo ya zura kwallo a raga - kuma wannan ne karo na biyu da Hojlund ya yi irin haka a wani lokaci da suka fafata da Portugal. dan wasa bitinha ne ya sake ci wa Portugal kwallo ta uku, sannan Joao Felid ya kara ta hudu a wasan da aka buga a birnin Copenhagen, kuma sakamakon ya bai wa Portugal damar samun maki uku. Kuma wannan ne karon farko da Portugal ta buga wasa tun bayan da Ronaldo mai shekara 41, wanda shi ne mafi zura kwallaye a tarihin kwallon kafar kasashe, ya bar sansanin kasar, bayan an ajiye shi a benci a wasan da suka yi da Norway. Bayan nasarar da suka samu a Denmark, kociyan tawagar ta Portugal, Jorge Jesus, mai shekaru 72 ya ce: "Akwai ‘yan wasa masu matsayi na musamman. Wannan abu ne a fili. Ya ci gaba da cewa "Amma zan sake fada - ka'idojin iri daya ne ga kowa. Wannan ita ce hanyar da na bi a duk tsawon aikina na horarwa, kuma zan ci gaba da bin ta." Sai dai a daren ranar da kociyan ya yi wannan maganar 'yar uwar Ronaldo, Elma Abeiro, ta rubuta a shafukan sada zumunta tun da farko cewa: "Cin amana abinci ne da aka fi jin dadinsa idan aka ci shi a hankali.’ Duk wanda yake bibiyar wasannin kwallon kafa ya san da cewa an shafe shekaru ana ganin kamar ba za a iya cire Ronaldo daga cikin tawagar ba bayan da ya ci wa Portugal kwallo 146 a wasanni 234. Sai dai a shekarun baya da kokarinsa ya ragu, an fara cece-kuce cewa watakila dan wasan Al-Nassr, wanda ya ci kwallo 979 jimilla a rayuwarsa ta kwallon kafa, yana hana tawagar yin abin da ya dace. ”Idan Na Yi Laifi A Hukunta Ni” - Ronaldo Cristiano Ronaldo ya ce bai yi ritaya daga buga wa tawagar Portugal wasanni ba, amma ya amince cewa ya kamata a hukunta shi saboda barin sansanin da suke sauka ba tare da izini ba. Kyaftin din mai shekara 41 ya bar sansanin Portugal bayan da ya kasance a benci ba tare da an yi amfani da shi ba a wasan da suka yi da Norway, sannan ya gano cewa ba zai fara karawa da Denmark ba a gasar Nations League. Ronaldo mai buga wasa a Al-Nassr, ya ci kwallo 146 a wasa 234 da ya buga wa Portugal, tare da taimaka wa kasar wajen lashe Euro 2016 da gasar Nations League sau biyu a tarihi. ...
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.